Ganawar Merkel da Mbeki a Pretoria | Siyasa | DW | 05.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ganawar Merkel da Mbeki a Pretoria

Mbeki da Merkel sun tattauna matsalolin Zimbabwe....

Merkel da Mbeki

Merkel da Mbeki

Acigaba da rangadin aikin da takeyi a nahiyar Africa,ayau ne shugabar gwamnatin Jamus ta gana da shugaba Thabo Mbeki na kasar africa ta kudu,kafin ta zaga domin ganewa idanunta gyare gyaren da akeyi na shirin gudanarda gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da zaayi a shekara ta 2010, a wannan kasa.

“Ina ma zaki zauna a wannan kasa fiye da kwanakin biyun da zakiyi?”wadannan sune kalaman shugaba Thabo Mbeki adeangane da bukatarsa na Merkel ta fadada wannan ragadi nata a africa ta kudu.

Shugabannin dai sun danyi raha adangane da wannan bukata,inda Mbeki ya kada da baki dacewa

“Wannan abu ne mai sauki,u,murni ne kadai da zaa fadawa masu lura da harkokin sufuri na filin jirgi,na cewa jirgin bazai tashi ba”

Sai dai a bangarenta Merkel tace hakan bazaiyi kyau wa Liberia ba,wadda nan ne inda zata wuce daga Africa ta kudun……..

Shugaba Thabo Mbeki da Angela Merkel a ganawar tasu dai,sun jadadda manufofinsu na ketare,inda Merkel ta sake mamaita jawabin da tayi a a headquatar kungiyar Africa a Adisa baba a jiya,adangane da manufar kafa sabuwar dangantaka tsakanin Africa da turai.Tace ya zamanto wajibi a ceto Africa daga matsalolin da take fama dasu,tare da hadin gwiwar samar mata tsaro,sai dai kuma dole kasashen na Africa su zage dantse wajen warware wadannan matsaloli nasu.

“Merkel tace mun tattauna batutuwan sinbabwe,kuma daga wannan tattaunawar tamu nasamu karin bayanai adangane da halin da ake ciki a wannan kasa,da kuma irin rawa da shugabbanin kasashen dake kudancin Africa ke takawa wajen gano bakin zaren warware shi.kuma a bangaren Africa ta kudu wadda ke fama dumbin yan gudun hijira na Zimbabwen,dole ta taimaka matuka wajen ganin cewa an cimma warware matsalolin.Halin da ake ciki a Zimbabwe yayi tsanani,kuma mai matukar muni kamar yadda na fada.Sai dai dukkan hakki ya rataya a wuyan shugaban kasar na warwaresu”

A nashi bangaren shugaba Thabo Mbeki yayi alkawarin cika da taka rawa a shiga tsakanin da yakeyi wajen daidaita kan bangarorin zimbabwen,inda yakara dacewa zai tabbatar da ad alci a zaben kasar da zai gudana a shekara mai gabatowa.Yace sauran kasashen Africa akar kashi AU na kokarin ganin cewa an kawo karshen take hakkokin jamaa da akeyi a Zimbabwe.

Adangane da furucin Prime ministan Britannia na kin halartan taron kasashen Africa dana Turai a watan Di samba a Lisbon idan shugaba Mugabe ya halarci taron kuwa,shugabar´gwamnatin jamus Angela Merkel tace wannan taro ne dake da muhimmanci wa kasashen na Africa,wanda kuma ya dace shugabannin nahiyar su bayyana..

“tace an dauki shekaru da dama ba tare da an gudanar da taro tsakanin Africa da Turai ba.Kuma kamar yadda na fada a kasa ta jamus,ina nan kan raayina na gayyatar dukkannin shugabannin Africa zuwa taron.Tace anan ne kowane shugaba zaizo yayi bayanansa,saannan sauran kasashe su mayar da martaninsu.Adangane da hakane nake jaddada cewar kowane shugaba yana da yancin halartan wannan taro”

Shugabannin biyu kazalika sun tattauna gasar kwallon kafa ta duniya da Africa ta kudun zata kasance mai masaukin baki a shekarata 2010,inda Merkel tayi alkawarin taimaka mata,kasancewar an gudanar da gasan na karshe a shekarrar data