1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar Livni da shugaba Abbas

Ministar harkokin wajen Izraela Tzipi Livini ta gana da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas ,a gefen taron inganta tattalin arziki na kasashen duniya dake gudana a birnin Davos dake kasar Switzaland.Dangane da wannan ganawar tasu Livni tace mataki na gaba adangane da samarda zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya,shine ganawar bangarori uku tsakanin shugaban Palasdinawa Abbas da prime minista Ehud Olmert na Izraelan da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza rice .Shugaba Abbas a nashi bangaren ya bayyana cewa bisa dukkan alamu shirin samarda zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu zai cimma nasara.