Ganawar Koffi Annan da Jan Pronck | Labarai | DW | 26.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar Koffi Annan da Jan Pronck

Nan gaba ayau ne, Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, Koffi Annan, zai gana da Jan Pronk ,Wakilin mussamman na Majalisar,a ƙasar Sudan wanda hukumomin Khartum, su ka yi wa kora kare, a wannan mako.

Kakakin Koffi Annan, ya ce, Sakatare Jannar na bada cikkaken goyan baya, ga Pronck, kuma har yanzu, ya da ɗaukar shi, a matsayin wakilin sa, a ƙasar Sudan.

A yammacin jiya, an gana tsakanin Koffi Annan, da sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condoleesa Rice, inda, ta bayana matsayin gwamnatin Amurika, a game da wannan batu.

Rice ta ce, ya zama wajibi, a Majalisar Dinkin Dunia, ta sake tura wakili cikin gagawa, zuwa Sudan, kuma ba wai lalle, sai Jan Pronck ba.

To saidai kamar yadda ta bayyana, Koffi Annan ke da wuƙa da nama, domin yanke shawara ƙarshe.

Idan dai ba a manta ba, gwamnatin Sudan, ta yanke shawara kora Jan Pronck daga ƙasar a sakamakon kalamomin da yayi, na cewar dakarun gwamnati, sun sha kayi har sau 2, daga ƙungiyoyin tawayen yankin Darfur.