Ganawar farko tsakanin Yayi Bonny da Denis Sassou N Guesso | Labarai | DW | 25.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar farko tsakanin Yayi Bonny da Denis Sassou N Guesso

Rikicin tawaye a kasar Tchad na ɗaya daga mahimman batutuwan da aka tantana kan su, tsakanin saban shugaban ƙasar Benin Yayi Bonny, da takwaran sa Denis Sassou N´guesso na Congo, wanda a halin yanzu ke riƙe da matasayin shugaban Tarayya Afrika.

An gana tsakanin shuagabanin 2, albarkacin ziyarar da saban shugaban Jamhuriya Benin ya kai, a birnin Brazaville jiya, litinin.

Yayi Bonny, da Denis Sassou N Guesso, sunyi Allah wadai da aniyar yan tawayen ƙasar Tchad ta ɗaukar mulki, tare da anfani da ƙarfin bindiga.

Sannan, sun yi kira ga ƙungiyoyi da ƙasashen Afrika, da su ci gaba,da ƙoƙari, domin cimma burin sassanta rigingimmun tawaye, a Cote ´ivoire ,da Jamhuriya Demkradiyar Kongo.

Kazalika, sanarwar ƙarshen taron tawagogin ƙasashen ,ta bayyana ƙara ƙarffafa hulɗoɗi tsakanin Benin da Kongo.