Ganawar Elbaradei da magabatan Iran | Labarai | DW | 13.04.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar Elbaradei da magabatan Iran

Shugaban hukumar kula da harkokin Nuclear na mdd mohammad Elbaradei,ya bayyana cewa har yanzu babu tabbacin cewa Iran ta sarrfa sinadran Uranium wanda ya kai kashi 3 da rabi bisa 100,wanda shina adadin wanda zaa iya samarwa domin cibiyoyin inganta makamashi.Yace a yanzu haka masu bincike sun dauki samfuri,kuma zasu gabatar dashi a gaban jamian gudanarwa na IAEA.Shugaban hukumar kula da Nuclear ta mdd yayi wannan furuci ne bayan ganawarsa da magabatan Tehran ayau,wanda ya biyo bayan ikirarin da kasar tayi na cimma sarrfa sinadran uranium wanda zai iya samar da ingantaccen makamashi,sabanin gargadin mdd.

Shima sakatare general na mdd Kofi Annan cewa yayi hakki ya rataya a wuyan iran ta tabbatar da duniya cewa bada mummunan manufa take gudanar da harkokin nuclearnta ba.

Kasashen turai da Amurka dai na zargin Tehran da shirin kera makaman nuclear,amma iran din tace shirin nucleanta na samarda da wutan lantarki ne.Hukumar kula da harkokin nuclear ta IAEA dai ta dauki shekaru 3 tana bincike shirin nuclean Iran din,amma har yanzu tace harkokin Iran din na makamashi ne,domin babu shaidan daya nunar dacewa tana kera makaman atom.

 • Kwanan wata 13.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6w
 • Kwanan wata 13.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6w