Ganawar David Cameron da Angela Merkel a Berlin | Labarai | DW | 21.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar David Cameron da Angela Merkel a Berlin

Matalolin faɗuwar darajar euro da karayar tattalin arzikin wasu ƙasashen Turai su ne suka mamaye tattaunawar shugabannin gwamnatocin biyu

default

Sabon priministan Britaniya David Cameron ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, a ziyararsa ta farko a birnin Berlin a matsayinsa na shugaban gwamnati. A taron manema labaru na haɗin gwiwa, Cameron da Merkel sun yarda da cewar daidaituwar kuɗin euro batu ne da dukkannnin ƙasashen Turai zasu yi maraba dashi, har da waɗanda basa amfani da euron. Sai dai shugabannin biyu sun samu saɓani akan tsaurin dokokin. Cameron yace ƙasarsa bazata  amince da kowane sauyi akan yarjejeniyar EU da zai daɗa janyo Britaniya zuwa cikin yankin euro. Shugaban gwamnatin Britaniya ya bada goyon bayansa wa shirin Merkel akan kasuwannin hada-hada, wanda za a tattauna a taron ƙasashen G20 masu cigaban masana'antu.

Mawallafiya: zainab Mohammaed Edita: Umaru Aliyu