1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Chirac da Merkel

Yahaya AhmedJanuary 24, 2006

Shugabannin biyu sun sadu ne don bude wani taron nuni kan birnin Dresden a garin Versaille da ke wajen birnin Paris. Sun kuma yi amfani da wannan damar ne wajen tattauna wasu batutuwan da har ila yau ske da bambancin ra'ayoyi a kansu.

https://p.dw.com/p/Bu2B
Shugaba Chirac da Angela Merkel
Shugaba Chirac da Angela MerkelHoto: AP

Shugaba Chirac da Angela Merkel sun yi wannan ganawar ne ba bisa manufa ba. Dalilin saduwarsu dai shi ne bude wani nunin da aka yi kan tarihin birnin Dresden a garin Versailles da ke wajen Paris. Amma duk da haka, sai da suka yi shawarwari kuma kan batutuwan da suka shafi harkokin siyasa. Sun dai bayyana cewa, za su yi duk iyakacin kokarinsu wajen ganin cewa, an sami ci gaba a wajen bunkasa manufofin siyasar Turai. A ran 14 ga watan Maris mai zuwa ne ministocin kasashen biyu za su yi wani taro a birnin Berlin, inda za su bayyana matakan da kasashen biyu ke niyyar dauka wajen cim ma wannan burin. Kamar yadda Merkel ta bayyanar:-

„Muna so ne mu aiwatad da hsirye-shiryen da Firamiyan Faransan ya gabatar a cikin jawabin da ya yi a wannan makon, a jami’ar Humboldt. Wato kamata ya yi, mu tsara manufofin da za su amince da halin rayauwar jama’a a nan Turai. Mun dai yi imanin cewa, idan Jamus da Faransa ba su jagoranci harkokin wannan nahiyar ba, to duk wasu manufofi na Turan ma gaba daya, wargajewa za su yi.“

kasashen biyu dai na kokari ne su yarje kan manufa daya, kafin taron koli na kasashen kungiyar EU da za a yi nan ba da dadewa ba. Ita Faransa dai na ganin cewa, kundin tsarin mulkin Turai da jama’an kasar suka yi watsi da shi a zaben raba gardamar da aka gudanar, wato ba shi da wani muhimmanci kuma gare ta. Tana kokari ne a halin yanzu, tag a yadda za a iya yin amfani da yarjejeniyoyin da ake da su yanzu, wajen hanzarta ci gaban al’amura a nahiyar. Jamus kuwa, har ila yau, tana mai ra’ayin cewa za a iya ceto kundin daga wargajewa. A huskar tattalin arziki ma , akwai bambancin ra’ayoyi tsakanin kasashen biyu. Faransan na son ta gabatad da shawarar rage wa kantunan sayad da abinci harajin nan na VAT ne, yayin da Merkel kuwa take adawa da hakan. A shawarwarin da suka yi dai, shugaba Chirac ya sake nanata matsayin kasarsa a kan wannan batun, inda kuma ya bukaci Merkel da ka da ta shure wannan shawarar gaba daya, a taron da ministocin kudi kasashen biyu za su yi yau.

Akwai dai wasu batutuwan da shugabannin biyu za su yi shawarwari a kansu, kamar dai rikicin da ake yi yanzu game da makamashin nukiliyan Iran. Jawabin da shugaba Chirac ya yi game da yin amfani da makaman nukiliyansa wajen afka wa kasashen da yi kira na `yan ta’adda dai, bai sami amincewar Jamus ba. Amma da yake amsa tambayar maneman labarai, shugaba na Faransa ya bayyana cewa:-

„Babu wani dalilin da zai sa wani ya ta da hankalinsa a Jamus a kan wannan batun.“

A nata bangaren Angela Merkel ta bayyana cewa, wajibi ne dai a bi wannan batun sannu a hankali, kuma, ya kamata a bi ta kan hukumar kula da makamshin nukiliya ta kasa da kasa, don tinkarar matsalar. Kuma kafin wata kasa ta dau wani mataki ma, sai dai ta jira tag a irin shawarar da kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya zai yanke tukuna.