1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Bush da Poutine.

July 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuHJ

Shugaban ƙasar Russie Vladmir Poutine, na ci gaba da ziyara aiki a ƙasar Amurika.

Ya yi ganawar farko da shugaba Georges Bush, a gidan sa dake Kennebunkport, inda kuma su ka yi doguwar tantanwa,cikin raha.

Shugabanin 2,sun yi masanyar ra´ayoyi a game da mu´amila tsakanin Russie da Amurika, wadda a halin yanzu ke fuskantar ƙiƙi-ƙaƙa.

Shugaba Bush ya sha zargin hukumomin Mosko, da take hakin demokarɗiya.

A nasa gwefen shugaba Vladmir Putine , ya turje tare da yin adawa da manufofin gwamnatin Amurika, a harakokin siyasa da na diplomatia a dunia.

Nan gaba a yau tawagogin 2 za su ci gaba da tantanawa, da zumar fido da sanarwar ƙarshen taro, wace zata bayyana sakamakon da su ka cimma.