1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar Bush da Kharzai a Camp David

Amurka da Afganistan sun cimma matsaya guda dangane da cewa bazaayiwa yan Taliban wani sassauci dangane da bukatar su saki bakin dan yan kasar Koriya ta kudu guda 21 da suke cigaba dayin garkuwa dasu ba.George W Bush da Hamid Kharzai a tattaunawar da suka gudanar yau a Camp David,sun amince dacewa babu ayayin tatauna batun sakin wayanda ake garkuwan dasu babu wasu sharudda da zaa gindaya.

Adangane da harkokin noman da fataucin tabar Wiwi da Afganistan ke fama dashi kuwa,Shugaba Bush yace zasu taka taimaka wajen shawo kann wannan matsala.