Ganawar bankwana tsakanin gwamnatin Schröder da shugaban kasa Host Köhler | Labarai | DW | 19.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar bankwana tsakanin gwamnatin Schröder da shugaban kasa Host Köhler

Haussawa kan ce dunia rawar yan mata na gaba ya koma baya.

Jiya ne a nan Jamus shugaban kasa Host Köhler yayi ganawar ban kwana da gwamnatin shugaban Geher Schröder.

An yi wanan haduwa jim kadan bayan da majalisar Bundestag ta zabi kakakin ta.

Geher Schröder da ya share shekaru 7 ya na shugabancin gwamnatin Jamus, ya kasance shugaban mai fain jinni da Jamusawa duk da tabatbarewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Schröder zai bar mukamnin na sa ga Angeller Merkell, ta Jam´iyar CDU, a sakamakon zaben yan majalisun taraya na ranar 18 ga watan da ya gabata.

Saidai Host Köhler, ya bukaci gwamnatin ta Schröder ta ci gaba da zaman wucin gadi ,na tsawan yan kwanaki, kamin sabuwar gwamnatin ta kama aiki gadan gadan.