Ganawar Annan da shugaba Assad na syria a Damascus. | Labarai | DW | 01.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar Annan da shugaba Assad na syria a Damascus.

Sakatare general na mdd wanda ke cigaba da rangadin aiki a yanmkin gabas ta tsakiya,yace ya samu tabbaci daga shugaba Bashar al-Assad na syria nacewa,Damascus zata dauki dukkan matakai da suka cancanta wajen tallafawa aiwatar da kudurin mdd akan kasar Lebanon.

Bayan tattaunawa da sukayi a birnin Damascus,Kofi Annan yace shugaban na Syria yayi alkwarin inganta harkokin tsaro da sintirin jamian tsaro akan iyakokin Lebanon da Syria,da nufin kawo karshen safarar makamai wa yan Hizbollah.Daga Damascus dai ,ayau din ne Mr Annan zai isa Qatar,kana gobe asabar ya isa kasar Iran.

 • Kwanan wata 01.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5g
 • Kwanan wata 01.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5g