1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Angela Merkel da Chirac a Rheinsberg.

YAHAYA AHMEDJune 6, 2006

Shugabar gwamnatin tarayyar Jamus, Angela Merkel da shugaba Jacques Chirac na Faransa, sun yi wani taron ƙoli yau a garin Rheinsberg da ke kusa da birnin Berlin, inda suka tattauna batun makomar kundin tsarin mulkin Ƙungiyar Haɗin Kan Turai.

https://p.dw.com/p/Btzr
Shugaba Chirac da Angela Merkel a taron maneman labarai bayan ganawarsu a Rheinsberg.
Shugaba Chirac da Angela Merkel a taron maneman labarai bayan ganawarsu a Rheinsberg.Hoto: AP

Tuni dai, an shafe shekara ɗaya, tun da al’umman Faransa suka hau kujerar na ƙi, a zaɓen raba gardamar nan da aka gudanar don amincewa da ko kuma yin watsi da kundin tsarin mulkin Ƙungiyar Haɗin Kan Turai. Sakamakon wannan zaɓen dai wani gagarumin kaye ne ga shugaba Jacques Chirac na Faransa. Amma duk da haka, ya dage kan bakansa na cewa, har ila yau wannan kundin dai na da makoma. Yana kuma kyautata zaton cewa, idan Jamus ta karɓi jagorancin Ƙungiyar EUn a farkon shekara mai zuwa, za a sake farfaɗo da batun.

A halin yanzu kam, ya sami ƙarfin gwiwa daga shugabar gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel, wadda, a cikin jawabinta ga taron maneman labarai bayan ganawar tasu, ta bayyana cewa:-

„Mun dai yarje kan sake farfaɗo da batun kundin tsarin mulkin, bayan tsawon lokacin da aka yi ta tunani a kansa. Idan Jamus ta karɓi akalar jagorancin Ƙungiyar EU, za mu sake maido da wannan batun a kan ajandarmu. Kafin wannan lokacin dai, za mu yi ta shawarwari, kan makomar kundin, mu tsara shirye-shirye kuma ta yadda za a sami dacewa, don bayan watanni 18, a daidai lokacin da Faransa za ta jagoranci Ƙungiyar, a cim ma yarjejeniya.“

Shugaba Chirac da Angela Merkel dai sun yarje kan cewar, bai kamata a ɗau tsawon lokaci wajen yin tunani kan kundin ba. Shugabana Faransan, ya kuma zargi masu adawa da shirin a ƙasarsa da yaudarar al’umma a lokacin yaƙin neman zaɓen, inda suka yi ta nanata cewa, akwai zaɓi ga kundin. Sai dai, inji shugaba Chirac:-

„A ƙashin gaskiya ba su da wani zaɓi. Ga shi dai ikirarin nasu yana janyo matsala yanzu. Duk da hakan dai, idan muka yi tunani mai zurfi kan batun, muka kuma tinkare shi da idon basira, za mu iya warware matsalar. Na yi imanin cewa, gwamnatin Jamus, za ta sake farfaɗo da wannan batun, idan ta karɓi jagorancin Ƙungiyar EUn a shekarar baɗi.“

To ko wace alƙibla Jamus ɗin za ta sanya a gaba game da wannan batun, idan ta fara jagorancin Ƙungiyar EUn? A halin yanzu dai, babu wata matashiya a kan hakan. Sai dai shugaba Chirac na mai ra’ayin cewa:-

„Yayin da muke ci gaba da yin tunani kan wannan batun, Faransa za ta iya ba da tata shawara, sa’annan Jamus kuma za ta auna ta ga yadda za a iya inganta kafofin Ƙungiyar Haɗin Kan Turan, ba tare da canza yarjejeniyoyin da aka cim ma ba.“

A nan dai Angela Merkel ba ta ce uffan ba tukuna. Masharhanta na ganin cewa, ba za a iya warware matsalar kundin tsarin mulkin Ƙungiyar EUn ba, sai lokacin da Faransa ta karɓi jagorancinta a cikin shekara ta 2008.

Kafin wannan lokacin kuwa, akwai taruka da dama da ƙasashe 25 mambobin ƙungiyar EUn za su yi ta yi don tattauna wannan batun.