Ganawar Abbas da Sarkozy
September 27, 2010Talla
Shugaban Fararansa Nicolas Sarkozy ya ce zai karɓi baƙuncin
shugabannin Isra'ila da na Palasɗinu a wata mai kamawa.
Sarkozy ya bayyana haka ne a yayin da yake neman ƙasashen
turai da ma ƙasashen da ke tekun Bahr - Rum da su taka
rawar gani wajen samar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta
Tsakiya.
Shugaba Sarkozy, wanda a yau ya karɓi baƙuncin shugaba
Mahmud Abbas na Palasɗinu, ya nemi ya san makomar
tattaunawar samar da sulhu a yankin na Gabas Ta Tsakiya da
aka riga aka fara. Ya kuma buƙaci a sake ɗage wa'adin gine-ginen Isra'ila da aƙalla watanni ukku zuwa huɗu.
Daga bisani dai Sarkozy ya ce shugaba Abbas, da firaministan Isra'ila
Benjamin Netanyahu da shugaban Masar Hosni Mubarak za su
ziyarci birnin Paris a watan Oktoba domin shirye - shiryen wani taron ƙoli
na ƙasashen tekun Bahr - Rum da za'a gudanar a watan
Nuwamba - idan Allah ya kaimu.
Mawallafiya : Pinaɗo Abdu
Edita:Umaru Aliyu