1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Schröder da Zapatero

November 9, 2004

A jiya litinin aka gudanar da ganawa ta farko keke-da-keke tsakanin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da takwaransa Zapatero na kasar Spain a garin Leon

https://p.dw.com/p/Bveo
Zapatero da Schröder a Leon
Zapatero da Schröder a LeonHoto: AP

Manufar ganawar tsakanin Schröder da Zapatero a garin Leon dake arewa-maso-yammacin kasar Spain na da nufin sake farfado da huldodin dangantakun kasashen biyu, wacce a zamanin baya tayi rauni sakamakon goyan bayan tsofon P/M Aznar ga matakin Amurka na yakar iraki da kuma Allah Waddai da wannan mataki da shugaban gwamnatin jamus Gerhard Schröder yayi. A cikin watan maris da ya wuce ne aka kifar da gwamnatin P/M Aznar mai ra’ayin mazan-jiya a kasar ta Spain. An dai lura da bushasha a fuskokin jami'an siyasar biyu a lokacin da suke hira da manema labarai bayan ganawar tasu. Schröder ya ce a halin yanzu al’amura na tafiya salin-alin a dangantakar Jamus da Spain. Shugaban gwamnatin ya kara da cewar:

A sakamakon azamarsa ta neman tuntubar juna da kuma magana tsakani da Allah P/M kasar Spain ya ba wa kasarsa wata sabuwar alkibla mai armashi a rawar da take takawa a manufofin Turai. Hakan abu ne da ya taimaka wajen tattaunawa a cikin gadin gaba, ko da kuwa an samu banbance-banbancen ra’ayi a tsakani.

A dai wannan marra da ake ciki yanzun banbance-banbancen ba su taka kara suka karya ba. Domin kuwa tun bayan da kasar Spain, a karkashin P/M Zapatero, ta zama ja gaba wajen tofin Allah tsine akan yakin Iraki da manufofin shugaba George W. Bush aka samu daidaituwar manufofi na ketare tsakanin Jamus da Spain. Kuma har yau, bayan sake zaben shugaba Bush da aka yi, Schröder da Zapatero na tattare da ra’ayin cewar matakai na soja kawai ba zasu tsinana kome wajen murkushe ta’addanci a duniya ba. Akan haka Zapatero ke gabatar da kira ga Kungiyar Tarayyar Turai yana mai cewar:

Karfafa hadin kai da musayar bayanai tsakanin kasashe shi ne kawai zai taimaka wajen bin wata manufa mai tasiri a fafutukar murkushe ayyukan ta’adda da sauran miyagun laifuka a sassa dabam-dabam na duniya.

An cimma daidaituwa tsakanin ministocin gida da na shari’a na kasashen biyu a game da hukumar bitar takardun rajistar miyagun laifuka bai daya da za a kafa tare da kasar Faransa a shekara mai zuwa. Kazalika ministocin tsaron na kasashen Jamus da Spain sun amince da karfafa hadin kai tsakaninsu a harkokin makamai, inda Jamus zata ci gaba da ba da hayar tankokin yaki na Leopard ga kasar Spain, sannan ita kuma Spain tayi alkawarin sayen makamai daga kamfanonin Jamus.