Ganawa tsakanin Schröder da Hariri a Berlin | Siyasa | DW | 20.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ganawa tsakanin Schröder da Hariri a Berlin

An gana tsakanin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da takwaransa P/M Lebanon Rafik Hariri a birnin Berlin, inda dukkan jami'an siyasar biyu suka hakikance cewar sai tare da tattaunawa tsakanin dukkan bangarorin da lamarin ya shafa ne za a kai ga warware rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya

Schröder da Hariri lokacin ganawarsu a Berlin

Schröder da Hariri lokacin ganawarsu a Berlin

Gwamnatin Jamus har yau tana kan bakanta a game da cewar shirin nan mai taken sabuwar taswirar zaman lafiyar Yankin Gabas ta Tsakiya, shi ne kadai zai kai ga warware rikicin yankin da ya ki ci ya ki cinyewa. Bayan ganawar da suka yi da P/M kasar Lebanon Rafik Hariri a birnin Berlin shugaban gwamnati Gerhard Schröder yayi nuni da cewar:

Bisa ga ra’ayinmu wajibi ne duk wata matsalar da za a tattauna kanta a fafutukar neman zaman lafiyar Yankin Gabas ta Tsakiya ta kasance akan turbar shirin nan na sabuwar taswirar zaman lafiya kuma bai dace wani bangare daya yayi gaban kansa domin zayyana wani abin da ransa ya raya masa ba.

Wannan furuci na Schröder tamkar hannunka mai sanda ne ga gwamnatin Isra’ila, wacce a bangare guda ta ce zata kakkabe matsugunan Yahudawa ‚yan kaka-gida a yankin zirin Gaza, amma a daya bangaren take neman ci gaba da fadada matsugunan a yammacin kogin Jordan. P/M Isra’ila Ariel Sharon ya samu goyan baya akan wannan matsayi nasa daga shugaban Amurka George W. Bush. Bisa ga ra’ayin Kungiyar Tarayyar Turai wannan mataki zai kai ne ga kwarar Palasdinawa. Schröder ya ce an samu dacewar baki tsakaninsa da takwaransa P/M Lebanon Rafik Hariri akan cewar ko da yake janyewar abu ne da ya kamata a yi madalla da shi, amma fa wajibi ne a ba wa Palasdinawa wata cikakkiyar dama ta tofa albarkacin bakinsu akan irin fasalin da matakin zai dauka. A nasa bangaren P/M Lebanon Rafik Hari ya ce wajibi ne Isra’ila ta janye daga dukkan yankunan Larabawa da ta mamaye sakamakon yakin shekarar 1967. Kazalika tilas ne kudurorin MDD su kasance tushen duk wani matakin da za a dauka domin warware rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya. Hariri ya kara da cewar:

Wajibi ne Isra’ila ta janye daga dukkan yankunan da take mamaya tun abin da ya kama daga shekarar 1967. Kuma a baya ga haka wajibi ne a dauki matakai na gaggawa domin samarwa da Palasdinawa kasarsu ta kansu.

P/M Lebanon ya ce ba ya zaton cewar Palasdinawa kimanin dubu 350 dake gudun hijira a Lebanon na kaunar zama dindindin a wannan kasa.

A kuma halin da ake ciki fadar mulkin Jamus a Berlin na bakin kokarinta wajen ganin an kira taron da aka kira na kusurwowi hudu da suka hada da wakilan Kungiyar Tarayyar Turai da na Amurka da Rasha da kuma MDD akan Yankin Gabas ta Tsakiya. Mai yiwuwa a gudanar da taron nan da karshen watan afrilu ko farkon watan mayu domin bitar halin da ake ciki a yankin. A dai mako mai zuwa ne shugaban kasar Isra’ila Mosche Katzav zai kawo ziyara Jamus kuma zai gana da shugaban gwamnati Gerhard Schröder.