Ganawa Tsakanin Schröder da Chirac | Siyasa | DW | 15.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ganawa Tsakanin Schröder da Chirac

A jiya litinin an gudanar da wata ganawa, ba a hukumance ba, tsakanin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da shugaban kasar Faransa Jacques Chirac a garin Aachen mai dadadden tarihi.

Schröder da Chirac lokacin ganawarsu a birnin Aachen jiya litinin

Schröder da Chirac lokacin ganawarsu a birnin Aachen jiya litinin

A ganawar tasu a garin Aachen mai dadadden tarihi, shuagabannin siyasar guda biyu, Schröder da Chirac sun fi mayar da hankali ne akan al’amuran Kungiyar Tarayyar Turai (KTT). Wannan ganawar dai, wacce tun misalin shekaru uku da suka wuce ne ake gudanar da ita bayan kowadanne makonni shida-shida tsakanin shuagabannin na kasashen Jamus da Faransa ta kasance mai muhimmanci ta la’akari da mummunan koma bayan da suka fuskanta a zaben majalisar Turai da aka gudanar a shekaran-jiya lahadi. To sai dai kuma dukkansu biyu sun ce suna kan bakansu na wanzar da matakansu na garambawul da jama’a ke kyama. Schröder ya ce wannan ba abin mamaki ba ne saboda matakai ne da suka tanadi tsuke bakin aljifun gwamnati dangane da yawan kudaden da take kashewa a al’amuran kyautata jin dadin rayuwar jama’a. Shugaban gwamnatin na Jamus sai ya kara da cewar:

Ba shakka ina jin radadin lamarin matuka ainun, amma duk da haka ba zata yiwu in janye daga wannan manufa ba, wacce take da muhimmanci matuka ainun a game da makomar Jamus baki daya. Ba zata yiwu in sa kafa in yi fatali da alhakin dake kaina a matsayin shugaban gwamnatin wannan kasa ba.

Shi ma shugaba Jacques Chirac ya dage akan ba da goyan baya ga matakan garambawul da P/Mnsa Jean-Pierre Rafferin ke dauka, saboda abu ne da ko ba dade ko ba jima zai taimaka a samu bunkasa mai dorewa ga tattalin arzikin Faransa da kuma samar da isassun guraben aikin yi ga jama’a a kasar. Dukkan shuagabannin biyu sun bayyana niyyarsu ta hadin kai domin cimma tudun dafawa akan dukkan batutuwan da za a tattauna kansu lokacin taron koli na yini biyu da shuagabannin kasashen KTT zasu gudanar a Brussels daga alhamis zuwa juma’a mai zuwa. To sai dai kuma sun ki su fito fili su bayyana mutumin da suke sha’awar ganin ya gaji shugabancin hukumar zartaswa ta KTT daga Romano Prodi mai barin gado. Dangane da maganar daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen Turai kuwa dukkan jami’an biyu sun dage akan bakansu game da danganta nauyin kuri’a akan yawan al’umar kasa a maimakon fadin harabarta kamar yadda kasashen Poland da Spain ke bukata. A karshen ganawar tasu ta jiya litinin shugaba Chirac ya mika godiya tare da bayyana jin dadinsa game da halartar shagulgulan samun shekaru 60 da kutsen da sojojin taron dagi suka yi a gabar tekun Normandie, bikin da aka gudanar a ranar shida ga wata. Chirac ya ce halartar shagulgulan da Schröder yayi wani lamari ne na tarihi dake tabbatar da kyakkyawan yanayi na zaman lafiya mai dorewa a nahiyar Turai.