Ganawa tsakanin Schröder da Blair | Siyasa | DW | 14.06.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ganawa tsakanin Schröder da Blair

A ganawar da suka yi da Schröder a Berlin P/M Birtaniya Tony Blair ya ce kasar ba zata yarda ta janye daga rangwamen da ake mata na gudaden gudummawa ga baitul-malin KTT ba

Gerhard Schröder da Tony Blair

Gerhard Schröder da Tony Blair

Ko da yake ya saki fuskarsa tare da fara’a a lokacin ganawarsa da takwaransa shugaban gwamnatin Jamus Gerhard schröder, amma P/M Birtaniya Tony Blair ya ci gaba da dagewa akan shawarar kin amincewa da soke sassaucin da ake wa kasarsa dangane da gudummawar da take bayarwa ga baitul-malin Kungiyar Tarayyar Turai. A lokacin da yake bayani game da haka Tony Blair cewa yayi:

Ko shakka babu game da cewar muhimmin abin da ake bukata shi ne kamanta adalci, amma wannan manufa wajibi ne da shafi dukkan bangarorin da kungiyar tarayyar Turai ke samun kudaden shiga. Domin kuwa kungiyar na fuskantar kalubala iri dabam-dabam a wannan karni na 21 da muke ciki. Maganar dake akwai shi ne, a nemo wata nagartacciyar hanyar da za a bi wajen tallafa wa kungiyar da isasshen kudi ta yadda zata iya tinkarar wannan kalubala.

Bisa ga ra’ayin Tony Blair, ci gaba akan manufar nan ta karya farashin amfanin noma, wacce ke cinye kashi 40% na kasafin kudin KTT, wacce kuma kasar Faransa ke cikin rukunin kasashen dake cin gajiyarta, ba abu ne da zai taimaka a kyautata hanyoyin samun kudaden shiga ga kungiyar nan gaba ba. A nasa bangaren shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya bayyanar a fili cewar faufau ba zai yarda a aiwatar da wani canji dangane da daidaituwar da aka cimma akan manufofin noma a shekara ta 2002, bayan famar kai ruwa ranar da aka yi tsakanin kasashen kungiyar ta tarayyar Turai ba. Wannan bayanin na mai yin nuni ne da barakar da ake fama da ita a halin yanzu haka akan kasafin kudin kungiyar da ake fatan zayyanawa daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2013, a tsakanin Birtaniya a bangare guda da sauran kasashen KTT a daya bangaren. Ita dai Birtaniya an kiyasce cewar bana zata yi tsumulmular abin da ya kai Euro miliyan dubu biyar sakamakon rangwamen kudaden gudummawar da ake yi mata bisa dalilin cewar bata cin gajiyar manufar karya farashin amfanin noman daidai da sauran kasashen kungiyar, kamar dai Faransa. Amma fa wannan alfarma da ake wa Birtaniya ta fara kai wa sauran kasashen KTT iya wuya, sabodda tana haddasa mummunan gibi ga kasafin kudinta kuma hatta kananan kasashe masu karamin karfi kamarsu Estoniya ko Hungary suna fama da radadin hakan. An saurara daga Schröder yana mai bayanin cewar:

Manufarmu ce a kayyade yawan kasafin kudi akan kashi 1% na jummular abubuwan da kasashen KTT ke samarwa a shekara. Amma a shirye muke mu yi kari akan haka domin kyautata makomar hadin kann Turai. A saboda haka ya zama wajibi sauran kawayenmu su nuna halin sanin ya kamata akan wannan manufa.

A dai halin da muke ciki yanzu babu wani karin bayani da za a iya yi akan wannan batu illa a saurara a ga yadda zata kaya a zauren taron kolin shuagabannin kasashen kungiyar a Brussels daga alhamis zuwa juma’a mai zuwa.