1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ganawa Tsakanin Schröder Da Barroso

A yammacin jiya alhamis shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya sadu da Jose Manuel Barroso shugaban hukumar zartaswa ta KTT dake jiran gado

Jose Manuel Barroso

Jose Manuel Barroso

Kamar dai yadda aka tsammata tun farko tambayar farko da manema labarai suka fuskanci jami’an biyu da ita ta shafi makomar Rocco Buttiglione ne, wani jami’an kasar Italiya da aka kuduri niyyar nadawa kantoman hukumar zartaswa ta KTT akan al’amuran cikin gida da na shari’a, wanda kuma ya fito fili yana mai la’antar ‚yan luwadi da kuma mata dake haifar ‚ya’ya ‚yan gaba da Fatiha. A lokacin da yake mayar da martani akan wannan tambaya Jose Manuel Barroso cewa yayi:

A dai wannan marra da muke ciki ba ma bukatar wani rikicin da zai ta da zaune tsaye, kuma na sikankance cewar zamu samu bakin zaren warware wannan matsala.

To sai dai kuma babu wani karin bayani da Barroso yayi a game da hanyoyin da za a bi a shawo kan wannan takaddama da ake yi. Ya ce ba zai yi wani bayani dalla-dalla ba, sai bayan da ya kammala ganawa da shuagabannin wakilan majalisar Turai a yau alhamis. Barroso ya kara da cewar:

Girmama ra‘ayin juna abu ne dake da muhimmanci a gare ni, amma fa duk da haka ba zan saduda ga manufofi na kabilanci ko wata wariya Ya-Allah ta jinsi ce ko ta addini.

Amma fa lafuzzan da aka ji daga bakin Buttiglione, mai zazzafan ra’ayin rikan sun haifar da rudami kuma jam’iyyu masu ra’ayin gurguzu da masu sassaucin manufofi da kuma masu fafutukar kare kewayen dan-Adam suka yi barazanar kifar da shi a lokacin da majalisar Turai zata gabatar da mahawarar nadinsa a ranar 27 ga watan nuwamba mai zuwa. Domin guje wa wannan tabargaza shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya gabatar da kira yana mai cewar:

Ina fatan cewar sabon shugaban da za a nada zai samu cikakken goyan baya tare da illahirin wakilan hukumarsa daga majalisar Turai. Muna bukatar wata kakkarfar hukumar zartaswa kuma Barroso ya bayyanar a fili cewar yana da ikon hada kan irin wannan kakkarfar hukuma. Jamus zata ba wa shugaban cikakken goyan baya ba tare da wata inda-inda ba.

Amma fa ‚yan jam’iyyun Socialdemocrats a majalisar ta Turai na bukatar ganin an ba wa Rocco Buttiglione wani mukamin dabam kuma ga alamu Barroso ya fara karkata zuwa ga wannan shawara, wadda mai yiwuwa ita ce zata taimaka a kawo karshen wannan sabani.