Ganawa Tsakanin Schröder, Chirac da Erdogan | Siyasa | DW | 27.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ganawa Tsakanin Schröder, Chirac da Erdogan

An gudanar da wata ganawa tsakanin shuagabannin kasashen Jamus, Faransa da Turkiyya, a fadar mulki ta Berlin domin musayar yau akan maganar karbar turkiyya a KTT

Erdogan, Schröder da Chirac

Erdogan, Schröder da Chirac

Manufar wannan ganawar dai ita ce bayyana iri kakkarfan hadin kan dake akwai tsakanin Schröder da Chirac akan wannan batu. An saurara daga bakin shugaban kasar Faransa Jaqcues Chirac yana mai bayanin cewar ra’ayi ya zo daya tsakaninsa da Schröder a game da karbar Turkiyya a KTT ko da yake zai dauki lokaci mai tsawo kafin hakan ya tabbata a nan gaba. Chirac ya kara da cewar:

Na yi imanin cewar karbar Turkiyya a KTT, babban alheri ne ga nahiyar turai da kuma ita kanta kasar ta Turkiyya, wannan maganar babu tababa game da ita, ko da kuwa lamarin zai dauki wasu shekaru 10 ko 15 ne masu zuwa. Wannan manufa alheri ce ga nahiyar Turai wajen tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya da mulkin demokradiyya, ba ma kawai ga nahiyar ba, har da sauran sassa na duniya.

To sai dai kuma shugaban na kasar faransa ya kara da yin nuni da cewar al’umar kasar, wadanda akasarinsu ke adawa da manufar karbar Turkiyyar, su ne zasu tsayar da wata shawara ta karshe ta hanyar kada kuri’ar raba gardama akan wannan batu. Babu wani takamaiman bayanin da Chirac yayi dangane da ranar da za a gabatar da shawarwari tare da kasar Turkiyyar, inda ya ce mai yiwuwa a wajejen shekara ta 2005. A nasa bangaren shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder, wanda ba ya da niyyar neman jin albarkacin bakin Jamusawa a game da wannan batu, nuni yayi da cewar dukkan kasashen Jamus da Faransa zasu ba da cikakken goyan baya a game da fara shawarwarin karbar Turkiyyar a lokacin taron kolin KTT a watan desamba mai zuwa. Da wannan bayanin Schröder ya sosa wa P/M Turkiyya Recep Tayyib Erdogan daidai inda ke masa kaikai, amma a daya bangaren ‚yan hamayya na Christian Union ba su ji dadin kalaman dake fitowa daga bakin Schröder da Chirac ba. Shugabar jam’iyyar CDU Angela Merkelk ba ta yi wata-wata ba wajen sukan lamirin ganawar da aka yi tsakanin jami’an siyasar guda uku. Ta ce bisa ga ra’ayin jam’iyyarta karbar Turkiyya a KTT wani ragon azanci ne kuma a saboda haka irin wannan ganawar ta kusurwa uku ba ta da alfanu. Abu mafi alheri shi ne a wayar da mutane a game da matsalolin da zasu biyo baya idan har Turkiyya ta zama cikakkiyar wakiliya a KTT. A karshen ganawar dai an gabatar da bikin rattaba hannu akan wata yarjejeniyar cinikin jiragen saman fasinja samfurin Airbus 36 da za a sayarwa da kamfanonin sufurin jiragen sama na kasar Turkiyya.