1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Schröder da Chirac

April 26, 2005

A yau talata a karo na biyar aka gudanar da taron ministocin kasashen Jamus da Faransa, inda aka yi amfani da wannan dama domin ganawa tsakanin Schröder da Chirac a birnin Paris

https://p.dw.com/p/BvcH
Schröder da Chirac
Schröder da ChiracHoto: AP

Ganawar tasu tayi kacibis da taron kwamitin ministocin kasashen biyu da aka shirya karo na biyar bisa manufar shawo kan al'’mar Faransa su goyi bayan daftarin tsarin mulkin bai daya tsakanin kasashen KTT. Taron manema labarai da ya biyo baya ya dauki wani fasali mai kama da yakin neman zabe domin neman goyan baya a kuri'ar raba gardama da Faransawa zasu kada akan daftarin tsarin mulokin bai daya tsakanin kasashen Turai. Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard schröder bai yi wata-wata ba wajen rufa wa shugaban Faransa Jacques Chirac baya a daidai lokacin da shugaban ke gabatar da kira ga jama’a da su yi na’am da daftarin tsarin mulkin, inda yake cewar:

Wannan daftarin tsarin mulki, ka gafarce ni shugaban gwamnati idan na karkata ga Faransawa, abu ne da zai taimaka wajen karfafa matsayin Faransa a nahiyar Turai ya kuma daga matsayin nahiyar kanta a siyasar duniya.

Ko da yake makonni hudu ne kacal suka rage kafin a kada kuri’ar ta raba gardama, amma akwai alamun cewar akasarin Faransawa ba zasu yi na’am da daftarin tsarin mulkin bai daya tsakanin kasashen KTT ba, saboda tsoron tasirinsa akan makomar jin-dadin rayuwarsu, musamman ma ta la’akari da matsalar rashin aikin yin da ta kai wa Faransar iya wuya yanzu haka. Masu adawa da kundin tsarin mulkin bai daya na ikirarin cewar in har an aiwatar da shi kasar zata fuskanci matsalolin da suka hada da tsuke bakin aljifun gwamnati akan kudaden da take kashewa wajen kyautata jin dadin rayuwar jama’a, da tauye albashin ma’aikata da rushe kafofi da dama na gwamnati, sannan su kuma kamfanoni na kasar su rika kwashe kudadensu na jari domin zubawa a ketare. Amma shugaba Jacques Chirac na bakin kokarinsa wajen musunta wannan zargi, inda ya ce kin amincewa da daftarin tsarin mulkin tamkar sake mayar da hannun agogo baya ne ga ci gaban da nahiyar turai ta samu akan hanyarta ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsarin mulki na demokradiyya a cikin shekaru 50 da suka wuce. A nasa bangaren shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya bayyana kwarin guiwar cimma nasarar kuri’ar ta raba gardama, amma ya ki ya ce uffan a game da abin da zai biyo baya idan har al’umar Faransa suka sa kafa suka yi fatali da wannan manufa ta hadin kan Turai.