1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

050310 Griechenland Deutschland Wirtschaftskrise

Tijani LawalMarch 5, 2010

A ranar juma'a aka shirya ganawa tsakanin shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel da P/M ƙasar Girka Giorgios Papandreou akan rikicin kuɗin ƙasar Girka

https://p.dw.com/p/MLXP
Masu zanga-zangar adawa da shirin tsumulmular kuɗi na gwamnati a GirkaHoto: AP

A dai halin da ake ciki yanzun ya zama wajibi akan ƙasar Girka da ta ɗauki tsauraran matakai na tsuke aljihun gwamnati domin kare makomar tattalin arziƙin ƙasar. A sabili da haka ne ma Firaminista Giorgos Papandreou ya zarce zuwa birnin Berlin yau juma'a domin ganawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a fafutukar neman goyan baya daga gre ta. Ƙasar Girka na buƙatar taimako daga ƙasashen Turai domin neman rance kuɗi akan kyawawan sharuɗɗa. A dai ranar litinin da ta wuce gwamnatin ƙasar ta gabatar da shirinta na tsumulmular kuɗi.

A haƙiƙa ba da sanarwar shirin na tsumulmular kuɗi ke da wuya sai dubban-dubatar 'yan ƙasar ta Girka suka runtuma zuwa tituna domin zanga-zangar adawa da shirin na gwamnati. A ƙoƙarinta na kare makomar baitul-malinta gwamnatin ƙasar Girka ta ba da sanarwar ɗaukar matakan da suka haɗa da rage albashin ma'aikatanta da kuma ƙara haraji kan kayan amfanin yau da kullum. Tsaffin masu fansho dai su ne zasu fi jin raɗaɗin waɗannan matakai saboda ba za a yi musu ƙarin kuɗaɗen fansho ba. A sakamakon haka ne suka shiga zanga-zangar ta adawa. Ga dai abin da wasu daga cikin su ke cewa:

Ya ce:"Wannan shi ne karo na uku a jere da aka ƙi yi mana ƙarin kuɗin fansho kuma a yanzun ma an wayi gari ne gwamnati na fafutukar ƙayyade yawan fansho mafi ƙanƙanta!"

"Bisa ta bakinsu babu kuɗin da za a ba wa masu fansho. To wai shin ina gudummawar fansho da muka yi shekara da shekaru muna bayarwa ta shiga?"

"A yanzu haka kowane mai fansho na ba da gudummawa ga matasa da ba su da aikin yi. Nine ke kula da ɗa na, wanda bayan aiki na tsawon shekaru 18 ya wayi gari baya da aikin yi. Wai shin wa zai kula da makomar jikokinmu, ya taimaka musu a makaranta da sauran harkokin rayuwa ta yau da kullum."

Gwamnati dai ta tsayar da shawarar gaggauta wanzar da waɗannan matakai, kuma ƙasar Girka ta ce ba ta buƙatar taimako ko da na sisin kwabo ne daga sauran ƙawayenta na Turai. Sai da firaminista Papandreou ya ƙara nanata hakan kafin isarsa Berlin domin ganawa da shugabar gwamnati Angela Merkel. Papandreou ya ce:

"Wajibi ne mu sake maido wa ƙasarmu amannar da tayi asararta. Wajibi ne akanmu mu nuna haɗin kai a cikin watanni masu zuwa domin mu tabbatar wa ƙawayenmu cewar ba mu dogara akan kowa ba, kuma a matsayinmu na ƙasa ɗaya al'uma ɗaya zamu iya ɗaukar ƙaddaranmu a hannunmu."

Jim kaɗan kafin ganawar tsakanin Papandreou da Angela Merkel, majalisar dokokin ƙasar Girka ta amince da shawarar tsmulmular kuɗin da gwamnati ta bayar. A kuma nan Jamus tuni gwamnatin ƙasar ta bayyana gamsuwarta da irin alƙiblar da Girka ta fuskanta game da ƙin dogaro akan taimako daga ƙetare. Matakan na gwamnatin Girka zata taimaka a yi tsumulmular abin da ya kai kusan Euro miliyan dubu biyar, lamarin da zai ba ta 'yar sararawa ta gajeren lokaci.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal    

Edita: Zainab Muhammed Abubakar