1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ganawa tsakanin Obama, Karzai da Zardari

Shugaba Barack Obama na Amirka ya gana da shugabanin Pakistan da Afganistan a cigaba da laluben hanyoyin samar da zaman lafiya a ƙasashen biyu.

default

Ganawar Obama da Karzai da Zardari

Shugaban Amirka Barak Obama, ya gana da shugaba Hamid Karzai na ƙasar Afghanistan, da kuma takwaran aikinsa na Pakistan, Asif Ali Zardari, inda suka tattauna sabuwar manufar Amirka ta neman hadin gwiwa tsakanin ƙasashen wajen yaƙi da da Taliban da kuma alƙa'ida.

Shugaba Obama na Amirka, ya gayyaci shugaba Karzai na Afghasnistan, da kuma shugaba Zardai na Pakistan zuwa birnin Washington ne, domin ƙarfafa sabon shirin da yake da shi ga ƙasashen biyu, dake maƙwabtaka da juna, waɗanda kowannensu kuma ke fuskantar tashin hankali daga masu tada zaune tsaye, wajen haɗa kai da nufin kawo ƙarshen ƙungiyoyin Taliban da alƙa'ida.

Bayan ganawar da suka yi, shugaba Obama ya ce yana mai farin cikin cewar dukkan shugabannin biyu sun yi na'am da irin munin barazanar da suke fuskanta, kana sun jaddada ƙudurinsu na yin aiki tare, domin tinƙarar ƙalubalen. Mr Obama ya ƙara da cewar:

Tilas muyi duk abinda ya dace wajen yin fito na fito da waɗanda ke son lalata Pakistan. Dole ne kuma mu tsaya tare da waɗanda ke ƙaunar gina Pakistan. Akan wannan dalili ne nema na bukaci Majalisar dokoki ta ci gaba da bayar da kuɗaɗen gina makarantu da hanyoyi da kuma asibitoci. Ina son al'ummar Pakistan su san cewar, ba wai kawai Amirka na yin adawa da masu tada tarzoma bane, a'a, tana tare da duk wani yunƙurin tabbatar da kyawawan abubuwan da suke fatan cimma.

Babban fatan shugaba Hamid Karzai shine daƙile ƙungiyar Taliba, wadda ke samun mafaka a wasu yankunan Pakistan saboda ayyukansu dake haddasa rashin daidaiton lamura a ƙasarsa. Shugaba Karzai, ya gabatar da tasa buƙatar ga al'ummar Pakistan:

Ina son 'yan uwanmu maza da mata dake Pakistan, su kwana da sanin cewar Afghanistan zata yi dukkan mai yiwuwa wajen samar da zaman lafiya da lumana a ƙasashen biyu.

Shi kuwa shugaba Asif Ali Zardari, wanda ke neman goyon bayan Amirka ta fuskar siyasa dana soji, yana gudanar da wannan tattaunawar ce a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar mutuwar jama'a sakamakon bata kashin da ake yi a yankin Swat, bisa matsin lambar Amirka, inda sojoji suka kashe aƙalla mayaƙan sa kai tamanin a yayin taho mu gamar da suka yi.

A watan Fabrairu ne wasu ƙasashen duniya suka yi ta suka ga gwamnatin Pakistan, saboda amincewar data yi na yin aiki da shari'ar musulunci a yankin Swat, mai yawan mutane miliyan ukku, suna masu cewar bada kai ne ga ƙungiyar Taliban, kasancewar matakin nasa bai kawo ƙarshen tashin hankali a yankin ba. A yanzu shugaba Zardari ya ce da alamar nasara:

Tsarin dimokraɗiyyar da Pakistan ta runguma zai ci gaba da wanzuwa, kana hadin gwiwar da muka yi zata kaimu ga nasarar akan masu tada tarzoma, kuma ganinan tare da Abokina shugaba Karzai, da kuma Amirka, muna bawa duniya tabbacin cewar, zamu yi aiki kafada da kafada da sauran ƙasashen duniya, wajen daƙile wannan annoba da kuma barazana.

A lokacin ganawar shugabannin ukku dai, Mr Obama ya nuna alhininsa ga fararen hular dake mutuwa sakamakon hare haren da sojojin Amirka ke kaiwa a ƙasar Afghanistan, inda ya ce Amirka da Afganistan, da kuma abokan ƙawancen su zasu gudanar da bincike, game da harin baya bayannan da yayi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama a lardin Farah na Afghanistan.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadissou Madobi