Ganawa tsakanin Merkel da Schüssel | Siyasa | DW | 02.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ganawa tsakanin Merkel da Schüssel

A jiya lahadi shugabar gwamnatin Jamus ta kai ziyarar mubaya'a ga takwaranta na kasar Austriya Wolfgang Schüssel

Merkel da Schüssel

Merkel da Schüssel

A lokacin da take jawabi shugabar gwamnatin ta Jamus ta ce Jamus da Austriya zasu yi hadin kai domin daga matsayin kungiyar tarayyar Turai (KTT). Sai dai kuma a ganawar da suka yi tare da takwaranta shugaban gwamnatin kasar Austriya Wolfgang Schüssel a lokacin wata liyafa ta cin abincin rana jami’an siyasar biyu sun mayar da hankalinsu ne kacokam akan batutuwan da suka shafi makomar KTT, suna masu watsi da matsaloli na siyasar kasa da kasa. Shugaban gwamnatin na kasar Austriya yayi amfani da wannan dama domin bayyana manufofin da kasarsa ta sa gaba dangane da shugabancinta ga KTT a cikin watanni shida masu zuwa, inda ya ci gaba da bayani yana mai cewar:

2.O-Ton Schüssel

Mun dauri niyyar ba wa kungiyar sabon jini a cikin watanni shida masu zuwa, saboda wannan lamari ne da ba makawa game da shi. Kuma akwai kyakkyawar turbar yin haka ta la’akari da abin da aka kasafta wa kungiyar dangane da shekaru bakwai masu zuwa. Sabuwar shugabar gwamnatin Jamus ta taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan manufa.

Wani abin lura a nan dai shi ne kasancewar kasar Faransa ta fara dari-dari da irin kusantar junan da ake samun tsakanin Jamus da Austriya. To ko Ya-Allah wannan hadin kai zai gurbata yanayin kawancen dake akwai tsakanin Jamus da Faransa. Dangane da haka Angela Merkel take cewar:

3.O-Ton Merkel

Akwai kyakkyawar dangantaka mai dadadden tarihi tsakanin Jamus da Austriya kuma a saboda haka maganar hadin kai ma bata taso ba. Austriya na daya daga cikin kasashen dake makobtaka da mu, kuma a saboda haka muke fatan ganin shugabancinta ga KTT ya samu nasara.

A cikin bayanin nata Merkel ta kara da cewar wajibi ne a dauki nagartattun matakai domin ta da komadar tattalin arzikin kasashen Turai. Kuma domin cimma wannan manufa wajibi ne a yi fatali da manufofi na dogon turanci, wadanda ba su da wata ma’ana.