1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Bush da Olmert

Yahouza Sadissou MadobiNovember 13, 2006

Shugaban Amurika Georges Bush ya tantana da Ehud Olmert

https://p.dw.com/p/BtxR
Hoto: AP

Praministan Isra´ila Ehud Olmert na ci gabada ziyara aiki a kasar Amurika.

Wannan itace ziyara ta 2, da Praministan Isra´ila, ya kai Amurika, tun bayan hawan sa kan karagar mulki, a watan Aprul na wannan shekara.

Ziyara ta Ehud Olmert na gudana, yan kwanakin ƙalilan, bayan da jama´iyar Geoges Bush, ta sha mummunan kayi a zaɓen yan majalisun Amurika.

A matakin farko, Olmert, ya gana da sakatariyar harakokin waje Condoleesa Rice,inda su ka tantana a game da batutuwa daban-daban da su ka shafi yankin gabas ta tsakiya, mussamman Iran da Iraki.

Kazalilka, ya gana da mataimakin shugaban ƙasa Dick Cheney, da yan majalisar wakilai, inda ya issar da godiyar yaduwa, a game da goyan bayan da su ke samu daga Amuika, mussamman bayan kujera naƙin da Amurika ta hau, a lokacin da komitin sulhu na MDD, ya buƙaci kaɗa ƙuri´ar yin Allah wadai ga Isra´ila, a game da hare haren da ta kai a zikrin Gaza, makon da ya gabata, wanda kuma su ka hadasa mutuwar Palestinawa kusan 20.

Cemma a kan hanyar sa, zuwa Amurika, Praministan Isra´ila, ya tabarwa manema labarai cewa, kayin da jam´iyar Republican ta sha, a zaɓen da a ka gudanar ranar talata da ta wuce, ba zai hadasa wani cikas ba, ga mu´amila tsakanin Amurika da Isra´ila.

Nan gaba a yau za a tantana tsakanin Ehud Olmert da shugaba Georges Bush a gfadar White House.

A wata hira da gidan talbajan na NBC, Ehud Olmert ya bayyana cewar ba zai taba amincewa ba kasar Iran ta mallaki makaman nuklea, ya kuma yi kira ga Amurika ta yi tsaye kan matasin ta na matsa kaimi ga hukumomin Teheran su yi wasti da aniyar su, ta ƙera makaman ƙare dangi, da ke matsayin babbar barazana, ga zaman lahia a yankin gabas ta tsakiya.

A dangane da rikici da Palestinu Olmert ya ce a shire ya ke ya ci gaba da tantanwa da Mahamud Abbas.

Na faɗi, na nanata, na kuma jaddada, a shirye nike, a ko wane lokaci ,in hau tebrin shawara tare da Palestinu domin shawo kan wannan baddala.

Bayan ganawa da shugaban Georges Bush yau komin dare Ehud Olmert zai tashi zuwa Los Angeles inda za shi halartar taron ƙungiyar bani yahudu mazauna Amurika.