Ganawa tsakanin alummar musulmi da jamian gwamnatin Jamus | Labarai | DW | 27.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawa tsakanin alummar musulmi da jamian gwamnatin Jamus

Wakilai daga alummomin musulmi 15 dake nan Jamus sun gana karo na farko da jamian gwamnatin Jamus a birnin Berlin.

Wannan dai shine karo na farko a jerin tattaunawa da aka shirya zaa rika gudanarwa tsakanin gwamnati da alummar musulmin Jamus cikin shekaru 2 zuwa 3 masu zuwa,tare da nufin mahawara kan batutuwa da suka shafe su.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Jamus Wolfgang Schäuble shi ya jagoranci tattaunawar,wadda akayi akan batutuwa kamar matsayin mata a musulunci da kuma alaka dake tsakanin gwamnati da addini.