1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa ta ƙarshe tsakanin EU da Iran a game da rikicin Nukiliya

March 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv69

Shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad yace matsayin da hukumar makamashin Nukili ta majalisar dinkin duniya IAEA ke ɗauka a kan ƙasar sa na da nasaba da harkokin siyasa. Mahmoud Ahmedinejad ya baiyana hakan ne a yayin ziyarar sa a ƙasar Malaysia. Yace abin takaici ne ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun rikide sun zama ƙungiyoyi na siyasa, kuma yan amshin shatan turawan yamma. Ahmedinejad yace Iran na buƙatar tattaunawa don samun masalaha amma ba za ta amince da dukkan wani yunkuri na tursasawa ba. A yau ne dai jamián ƙasashen ƙungiyar tarayyar turai zasu gana da jamián ƙasar Iran a matakin ƙarshe kafin hukumar makamashin nukiliyar ta gudanar da taron a ranar litinin mai zuwa domin ɗaukar mataki da zai iya kaiwa ga gabatar da Iran a gaban kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya. Tattaunawar da ta wanzu a baya, tsakanin Iran da Rasha bai cimma wata nasara ba. ƙasar Rasha ta yiwa Iran tayin sarrafa mata makamashin nukiliyar domin kawar da shakkun da ake baiyanawa cewar Iran na shirin kera makamin nukiliya. A hannu ɗaya dai ƙasashen turai da Amurka na zargin Iran da yunƙurin mallakar makamin ƙare dangi, batun kuma da Iran din ta musanta.