Gambiya ta haramta gangamin bayan zabe | Labarai | DW | 30.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gambiya ta haramta gangamin bayan zabe

Shugaba Yahya Jammeh na kasar Gambiya ya sanar da cewar ba za'a yarda da wani gangami a kasar ba bayan makonni biyu na yakin neman zabe

Shugaba Yahya Jammeh na kasar Gambiya ya sanar da cewar ba za'a yarda da wani gangami a kasar ba bayan makonni biyu na yakin neman zabe. Sanarwar na zuwa ne yini guda bayan gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaban adawa Adama Barrow a babban birnin kasar wato Banjul.

Boren 'yan adawar na ranar wannan Talatar, na bayyana rarrabuwar kawunan da nuna gajiyawar jama'a game da shugabancin shekaru 22 na Jammeh  akan karagar mulki. Sai dai shugaban ya ce abokin takararsa ba zai yi nasara ba. 

Hamshakin dan kasuwa a Gambiya, Barrow ya kasance dan takarar da ke wakiltar dukkan jam'iyyun adawar kasar, bayan kamun kazar kuku da aka yi wa magoya bayansa a wata zanga-zanga mafi girma na adawa da gwamnati da aka gudanar a watan Afirilu. 

Duk da cewar babu kuri'un jin ra'ayin jama'a a hukumance, majiyar diplomasiyya na nuni da cewar wannan shi ne karo na farko da Yahya Jammeh ya samu mai kalubalantarsa da ke da karfi tun da ya dare karagar mulki a shekara ta 1994.