Gambiya: Sojoji sun kwace iko da cibiyar hukumar zabe | Labarai | DW | 13.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gambiya: Sojoji sun kwace iko da cibiyar hukumar zabe

Sojojin Gambiya sun kwace iko da cibiyar hukumar zabe ta kasar a daidai loakcin da wata tawagar shugabannin kasashen Afirka ke ganawa da Shugaba Jammeh a birnin Banjul.

Rahotanni daga kasar Gambiya na cewa sojoji sun kwace iko da babban ofishin hukumar zabe ta kasar a safiyar wannan Talata. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tawagar wasu shugabannin kasashen Afirka a karkashin jagorancin shugabar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ta gana da Shugaba Yahya Jammeh da ma sabon shugaban kasar mai jiran gado Adama Barrow a birnin Banjul a wani yinkuri na shawo kan shugaban wanda ya sha kayi a zaben ranar daya ga watan Disamba da ya yi hakuri ya mika mulki. 

Tawagar wacce ta kunshi Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Ernest Bai Koroma na Saliyo da John Mahama shugaba mai barin gado na kasar Ghana ta isa a kasar ta Gambiya ne a bisa bukatar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ta CEDEAO ko ECOWAS. 

Bayan kammala ganawar tasu  rahotanni sun ruwaito Shugaba Buhari na Najeriya na cewa Shugaba Jammeh ya basu hadin kai ba tare da ya yi wani karin bayani ba kan takamaiman abinda tattaunawar tasu ta cimma.