Gambiya: Sabon bikin rantsar da Adama Barrow a Banjul | Siyasa | DW | 17.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gambiya: Sabon bikin rantsar da Adama Barrow a Banjul

Shugaba Barrow da ya gaji dan kama karya Yahya Jammeh, zai fuskanci kalubale wajen tayar da komadar tattalin arzikin kasar da kuma batun hada kan 'yan Gambiya bayan rabuwar kanun da aka fuskanta.

Gambias Präsident Adama Barrow während einer Pressekonferenz in Banjul (Reuters/T. Gouegnon)

Shugaba Adama Barrow lokacin wani taron manema Labarai

Shi dai Adama Barrow ya fara rantsuwar kama aiki a ofishin jakadancin Gambiya da ke Senegal a tsakiyar watan Janairu, saboda Yahya Jammeh da ya doke a zaben shugaban kasar ya ki sauka daga karagar mulki. Sai da sojojin kawancen na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO suka yi yunkurin amfani da karfin tuwo wajen saukar da shi, sannan Jammeh ya amince da yin hijira zuwa Eqauatorial Guinea.

Gambia Präsident Adama Barrow (picture alliance/abaca/X.Olleros)

Shugaba Adama Barrow na Gambiya

Kokarin kawo sauyi a kasar Gambiya

Sabon shugaban na Gambiya ya yi alkawari kawo sauyi a fannin siyasa, saboda a yanzu 43 daga cikin 'yan majalisa 48 na kasar sun fito ne daga jam'iyyar Yahya Jammeh. A wannan hali dai Adama Barrow ba zai iya aiwatar da manufofin da ya sa a gaba ba. Dama kuma kawunan 'yan Gambiya sun rabu bayan rikicin shugabanci da aka samu a baya-bayannan. Peter Penar, Malami ne a jami'ar Michigan ta Amirka da ya kware kan siyasar Gambiya ya ce da jan aiki a gaban Shugaba Barrow.

"Shugaba Barrow na da kalubale a fannoni da dama: dole ne ya hada kan 'yan kasar bayan rikicin da aka fuskanta da ya kai ECOWAS tilasta wa tsohon shugaba sauka daga mulki. Ya hau mulki a wani yanayi na rarrabuwar kawuna, a yanayin da majalisa take mamaye da 'yan jam'iyyar da a baya ke rike da madafun iko ta APRC."

Jam'iyyar Jammeh na da sauran fada a ji

Gambia Wahlen Yahya Jammeh (picture alliance/AP Photo/J. Delay)

Tsohon Shugaban Gambiya Yahya Jammeh

Adama Barrow ba zai samu akaifar susa ba matikar jam'iyyar Yahya Jammeh na ci gaba da fada a ji a harkokin majalisar dokokin Gambiya. Dalili kuwa shi ne ana zargin gwamnatinsu da ta shude da tauye hakkin bil-Adama da na fadin albarkacin baki tare da azabtar da abokan adawa. Saboda haka da kamar wuya wadannan 'yan majalisa su bashi hadin kan da yake bukata. Hasali ma dai ba a san ta'asar da za su iya aikatawa ba. Ko a ranar Jumma'ar da ta gabata sai da aka kama daya daga cikin dogaran tsohon shugaba Jammeh da bindiga a masallacin da sabon shugaba Adama Barrow ke sallar Jumma'a. Saboda haka ne Peter Penar na jami'ar Michigan ya ce tsawaita wa'adin rundunar sojin kasashen yammacin Afirka zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a Gambiya:

ECOWAS na taka rawar gani a Gambiya

"ECOWAS ta dauki matakin da ya dace a ganina, saboda bayan rikici sojojinta sun ci gaba da zama don tabbatar da tsaro a babban birnin Gambiya. Wannan abu ne mai kyau domin zai sa a samu kwanciyar hankali. Amma idan sojojin suka janye, ayar tambaya a nan ita ce me magoya bayan Jammeh za su aikata idan babu matakan tsaro."

Wani batu da ke ci wa Barrow tuwo a kwarya shi ne na hulda tsakanin Gambiya da sauran takwarorinta na duniya. Shi dai wanda ya gabaceshi ya katse hulda da kungiyar Commonwealth tare da fitar da kasar daga kotun ICC. Sannan Kungiyar Tarayyar Turai ta katse duk taimakon da take bai wa Gambiya tun shekara ta 2014, alhali tallafin da EU ke bai wa Gambiya na da matikar muhimmanci ga tattalin arzikin kasar. Kanfanonin Gambiya sun durkushe sakamakon dimbin bashin da ke kansu. Sannan 'yan kasar na hijira saboda rashin aikin yi.

Sauti da bidiyo akan labarin