1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gamayyar ƙasa da ƙasa na ci gaba da yunƙurin kai wa waɗanda girgizar ƙasar nan ta shafa a Indonesiya taimakon agaji.

May 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuwH

Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar ba da taimakon agaji ta Red Cross ta ƙasa da ƙasa, na jagorancin wani gagrumin yunƙurin da ƙungiyoyin sa kai da na ba da taimakon agaji ke yi wajen ƙara kai taimako cikin gaggawa, ga waɗanda mummunar annobar nan ta girgizar ƙasa ta shafa a ƙasar Indonesiya. A halin yanzu dai, jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Geneva, sun ce ana ta samun taimako daga sassa daban-daban na duniya, tun abin da ya kama daga Beijing zuwa Washington, da kuma London zuwa Sydney.

A kan tsibirin Java, a ƙasar ta Indonesiya, inda girgizar ta auku a ran asabar da ta wuce, jami’an ceto da na ba da taimakon agaji da ke ta aiki ba ƙaƙƙautawa, musamman a garin Yogyakarta, inda girgizar ta fi muni da kuma ɓarna, sun ce abin da suka fi bukata yanzu cikin gaggawa ne, asibitocin tantuna na wucin gadi, inda za a yi wa waɗanda suka ji rauni jiyya, da kuma kayayyakin tabbatad da tsabta da inganta ruwan sha.

Kawo yanzu dai, kusan mutane dubu 5 ne aka ƙiyasci cewa girgizar ta halaka, sa’annan dubanni kuma sun ji rauni, yayin da wasu mutane kimanin dubu ɗari biyu kuma suka rasa matsugunansu, sakamakon wannan girgizar mai ƙarfin awo 6 da ɗigo 3 a kan mizanin Richter.