1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gamaiyar Yahudawa a Jamus

A wannan makon ake tunawa da ta´asar da aka aikata kan Yahudawan Jamus shekaru 70 da suka wuce.

default

Bikin Chanukka a gamaiyar Yahudawan Hameln

A daren tara zuwa 10 ga watan Nuwamban shekarar 1938 a faɗin Jamus gaba ɗaya aka ƙaddamar da hare hare akan Yahudawa da ƙone wuraren ibadarsu da kantunansu da dukkan abubuwa dake da nasaba da Yahudanci. Wannan dai shi ne mafarin kisan ƙare dangi da aka yiwa Yahudawa a nan Jamus a lokacin yaƙin duniya na biyu da nufin kawad da jinsunansu daga doron ƙasa. A wannan makon gamaiyar Yahudawa a nan Jamus ta ke zaman juyayi na cika shekaru 70 da aikata wannan ta´asar akansu. Shirin na yau dai zai duba faɗin tashin da Yahudawa suka sha tun daga wancan zamani har izuwa wannan rana ta yau.

Wata gamaiyar Yahudawa dake a wani ƙaramin gari da ake kira Hameln, inda tun kimanin shekarau 400 da suka wuce aka kafa wannan gamaiya. Su ma Yahudawan wannan yanki kamar takwarorinsu a faɗin Jamus gaba ɗaya ba su tsira daga ta´asar ranar daren tara zuwa 10 ga watan Nuwanban shekarar 1938 ba. Amma yanzu shekaru gwammai bayan haka rayuwar Yahudawa ta fara haskakawa a garin na Hameln. Kamar a ko-ina cikin Jamus a wannan garin ma Yahudawa daga tsohuwar tarayyar Sobiet sun samu sabuwar damar farfaɗo da addini da kuma al´adarsu. A halin nan ma da ake ciki mazauna a Hameln na tinƙaho da wannan ci-gaba da aka samu.

Wannan waƙa da yara suka rera mai taken Gabriel na matsayin wani fatan alheri ga makomar gamaiyar Yahudawan Hameln wadda ɗaukacin mabiyanta tsofaffi ne.

Wannan dai wata yarinya ce mai suna Miriam ta na karanta littafin Attaura. Miriam kamar sauran yaran Yahudawa tana koyon harshen Hebrew a wajen Peter, ɗalibi wanda a ƙarshen mako yake kula da wani rukuni na ƙananan yara.

“Ina karatu ne a fannin koyon harsunan Ingilishi da Sipaniyanci a garin Paderborn. Amma ina zuwa nan wurin don yin ibada da kula da ƙananan yara. Rayuwa a wannan gamaiya musamman ta addini ta na da muhimmanci. A matsayina na Bayahude ba zan iya rayuwa ba tare da wannan gamaiya ba. Ina buƙatar wannan gamaiya ba kawai domin addini ba, a´a ta na matsayin wani abin dogaro. Hakan na da muhimmanci a garemu.”

Kimanin shekaru 10 da suka wuce wata ƙaramar ƙungiyar Yahudawa da suka yo ƙaura daga Rasha da kuma wata ´yar Amirka suka kafa wannan gamaiyar ta Hameln. Wannan ba-amirkiya mai suna Rahel Dohme wadda tun a shekarar 1982 ta ke zaune a nan Jamus ita ce shugabar wannan gamaiya.

“A shekarar 1997 muka kafa wannan gamaiya. Wannan lokacui na da matuƙan muhimmanci a gareni. Da farko dai ba mu da yawa. Muna haɗuwa ne a matsayin wani gungu na Yahudawa muna ibada a cikin falo na.”

Daga baya sun yanke shawarar kafa wata gamaiya ta masu sassaucin ra´ayi wato abin nufi maza da mata za su riƙa yin ibada tare. Wani lokaci mace ce ke jagorantar aikin ibadar wanda ya haɗa da kiɗa wanda a cikin wannan addini yake taka muhimmiyar rawa. Rahel Dohme ta na farin ciki ganin yanzu ba tsofaffi ne kaɗai ke halartar wurin ibadar ba.

“Yara da matasa na halartar wurin ibabar. Ko da yake ba su da yawa amma bisa la´akari da yawan membobinmu za a samu gagarumin ci-gaba nan ba da jimawa ba. Bayan an tarwatsa mu a Jamus yanzu sannu a hankali Yahudawa sun fara haɗa kai. Dukkanmu Yahudawa sun fito ne daga ƙasa ɗaya, al´ada ɗaya bisa dokokin addininsu. To amma da farko waɗanda suka zo nan ba su san addinin ba.”

Daga cikin mutanen da ke ɗaukar mafakar da suka samu a garin Hameln a matsayin wata sa´a akwai Josif da Polina.

“A lokacin da nake tarayyar Sobiet ni ba ruwa na da addini. Na samu tarbiya ce ta wanda ba ruwansa da addini. A makaranta da jami´a aƙidar Markisanci na koya. Saboda haka a nan na fara koyan addini tun daga tushen sa.”

Ita kuwa Polina cewa ta yi:

“Zuwa na Jamus wani abin alheri ne gareni. A duk lokacin da aka tambaye ni ko na gamsu da zama na a Jamus, cewa na ke yi gamsuwata a Jamus ita ce damar tafiyar da rayuwa ta a matsayin bayahudiya. Ban samu damar yin haka ba a Rasha.”

Dukkansu biyu suna halartar bukin ibadar Yahudawa na Sabbat a wannan gamaiya, inda sukan rera waƙoƙi sannan daga bisani su ci abinci tare.

A kan yi ibadar ne a cikin harsuna biyu. A kullum ana fassara addu´o´in a cikin harshen Rasha, wanda Irina Pelz mai kula da sashen jin daɗin jama´a na gamaiyar ke yi. Irina ´yar asalin ƙasar Ukraine tana taimakawa sabbin zuwa da shawarwari da sauran abubuwa da ba a rasa ba.

"Aiki na dai shi ne yiwa membobin wannan gamaiya rakiya wurin hukumomi. Inataimakawa wajen rubuce rubuce wato kamar rubuta wasiƙu ga jami´ai da fassara. Ina kuma yi musu rakiya wajen likita da da neman gidajen haya musamman wuraren da ake buƙatar mai jin Jamusanci."

Ko da yake har yanzu suna gudanar da ayyukan ibadar ne a cikin wani karamin ɗaki amma bisa ga dukkan alamu hakan zai canza domin suna fatan gina ɗakin ibada irin na Yahudawa nan ba da jimawa ba, inji Rahel Dohme shugabar gamaiyar ta Hameln.

"A kullum muna tattare da kyakkyawan fata. Kasancewarmu Yahudawa mun yi imani da samun kyakkyawar makoma. Ina tsammanin jama´ar wannan garin sun san cewa ana rashin wani wurin ibadar Yahudawa. Saboda haka za a yi ƙoƙarin ganin sabo tun da a da ma an taɓa yi wani a shekarar 1879."

Sauti da bidiyo akan labarin