Gamaiyar Jamiyun yan shia tace a shirye take ta dakatar da takarar al Jaafari | Labarai | DW | 11.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gamaiyar Jamiyun yan shia tace a shirye take ta dakatar da takarar al Jaafari

Jamiyar Fadhila cikin gamaiyar jamiyun yan shia a Iraqi tace a shirye take ta zabi wani dan takara da zai maye gurbin Firaminista Ibrahim al-Jaafari,muddin dai gamaiyar jamiyun ta gagara sasanta wannan batu.

Ana sa ran gamaiyar jamiyun yan shiar zata soke sunan Jaafari a matsayin dan takararta na matsayin firaminista cikin sabuwar gwamnati,saboda matsin lamba da take samu daga bangarorin yan siyasa na sunni da Qurdawa,sai dai kuma akwai yiwuwar soke takarar al Jaafari zai rabe gamaiyar jamyiun na yan shia gida 2.