Gagarumin farmakin soji a Afghanistan | Siyasa | DW | 16.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gagarumin farmakin soji a Afghanistan

Dakarun NATO na cigaba da kutsawa lardin Helmand cikin taka tsantsan.

default

Sojin ISAF a lardin Helmand a kudancin Afghanistan

A gagarumin farmakin da suka ƙaddamar tun bayan faɗuwar gwamnatin Taliban a shekarar 2001, dakarun sojin NATO na kutsawa lardin Helmand inda suke fafatawa da mayaƙan Taliban. Sai dai dakarun na NATO na yin taka tsantsan saboda nakiyoyin da yan Taliban ɗin suka binne a ƙarƙashin ƙasa a yankin Marjah dake kudancin Afghanistan.

Fatan da ake da shi ga wannan farmaki shine sauya fasalin alámura tare da kakkaɓe yan tawayen Taliban a yaƙin da aka shafe fiye da shekaru takwas ana gwabzawa dasu. Gagarumin farmakin har ila yau na zama zakaran gwajin dafi na sabbin dabarun da gwamnatin Barack Obama wanda ke shirin tura ƙarin sojoji zuwa ƙasar ta Afghanistan a wannan shekarar ta 2010 da kimanin dakarun soji 35,000. Mai baiwa Obama shawara kan harkokin tsaro Janar James Jones yace wannan loakaci mai muhimmanci na ɗaukar mataki.

" Wannan shine karon farko da muka sanya dukkanin matakai na sabbin dabarun shugaba Obama".

Afghanistan / US-Soldaten / Helmand / NO-FLASH

Sojojin Afghan dana gamaiyyar ƙasa da ƙasa tare da NATO ke sintiri a ƙauyen Qari Sahib dake lardin Nad Ali a gundumar Helmend.

Tun a cikin watan Disambar bara ne dai Obama ya gabatar da sabbin manufofin da kuma dabarun da zaá aiwatar don cin nasara a Afghanistan. Muhimmai daga cikinsu sun haɗa da samar da ƙarin sojoji da samar da ƙarin kuɗaɗe na taimakon agaji ga ƙasar.

Janar Jones yace tun daga ranar Asabar  da ta wuce haɗin giwar sojojin ƙawance kimanin 15,000 tare da sojin Afghanistan suka shiga lardin Helmand a ƙoƙarin ƙwace ragamar wannan wuri daga hannun yan Taliban.

" A maimakon yadda a baya muka riƙa barin wuri bayan mun kawar da yan Taliban, manufarmu a yanzu ita ce zamu riƙe yankin bayan mun kakkaɓe yan tawayen sannan mu samarwa alúmar gine gine da tsaro mai inganci da kyakyawar gwamnati inda daga ƙarshe zaá sami cikakken yanci na yan Afghanistan waɗanda zasu ƙarɓi ragamar gudanarwa a waɗannan wurare".

Sai dai kuma babbar ayar tambayar ita ce shin sojin Afghanistan ɗin zasu iya riƙe yankin bayan sojin Amirka sun bar wurin ? Anya gwamnatin Karzai zata iya samar da daidaito da kwanciyar hankalin da ake buƙata a yankunan waɗanda ada suke ƙarƙashin Taliban ? da dama dai suna baiyana shakku kamar yadda wata yar jarida Atia Abawi dake tare da rundunar sojin Amirka a yankin ta baiyana.

Afghanistan / Offensive / Helmand / Mardscha

Jirgin saman sojin Amirka ke shawagi a sararin samaniyar Marjah a gundumar Helmand

" Mafi yawancin faɗan da ake gwabzawa a zancen da nake yanzu, sojojin Amirka ne suke yinsa, sune suke jagorantar komai kuma sune akan gaba".

Ana iya cewa dai har yanzu akwai jan aiki a gaban yan Afghanistan kafin su yi wani tasiri na azo a gani a ƙasarsu. Ko da yake suna da sauran lokaci daga nan zuwa tsakiyar shekara mai zuwa lokacin da Obama yake fatan fara maido da sojojinsa gida idan alámura suka inganta.

A waje guda kuma a wani farmakin haɗin gwiwa na Pakistan da jamián leƙen asirin Amirka sun sanar da cafke wani kwamandan yan Taliban Abdul Ghani Baradar a birnin Karachi na ƙasar Pakistan kuma ana cigaba da yi masa tambayoyi. Rustam Shah Mohammed tsohon jakadan Pakistan a Afghanistan yace kama Abdul Ghani Baradar nasara ce babba.

" Wannan babban koma baya ne ga yan Taliban. Mullah Baradar shine jamií na biyu mafi girma a ƙungiyar Taliban, kwamanda ne wanda ya sami gogewa sosai. A saboda haka kama shi da aka yi zai yi tasiri matuƙa wajen karya lagon yan Taliban".

Mawallafa : Engelke, Anna / Abdullahi Tanko Bala