Gabon: Bude taron sasanta rikicin siyasa | Labarai | DW | 28.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gabon: Bude taron sasanta rikicin siyasa

Shugaba Ali Bongo na Gabon a wannan Talatar ya bude taron sansanta rigingimun siyasar kasar a wani mataki na neman kashe wutar rikicin siyasar da ta taso bayan zaben watan Agustan da ya gabata mai cike da cece-kuce.

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya bude a wannan Talata taron sansanta rigingimun siyasar kasar a wani mataki na neman kashe wutar rikicin siyasar da ta taso a kasar bayan zaben shugaban kasa na watan Agustan da ya gabata mai cike da cecekuce. 

Taron wanda aka bude a karkashin jagorancin Shugaba Ali Bongo a fadar shugaban kasar da ke a birnin Libreville, ya samu halartar wakillan gwamnati da na wasu jam'iyyun siyasa akalla 50, da na kungiyoyin farar hula sama da dubu da 200, dama  kuma jami'an diplomasiyya. 

Sai dai madugun 'yan adawar kasar Jean Ping wanda ke ci gaba da ikrarin lashe zaben watan na Agusta da magoya bayansa, sun kaurace wa taron wanda za a kwashe makonni ukku ana gudanar da shi. 

Taron zai gudanar da nazari kan batutuwa da dama da suka hada da irin sauye-sauyen da hukumomin jamhuriya suke bukata, da gyaran kundin tsarin zabe da kotun tsarin mulki da dai sauran batutuwa da za su taimaka ga karfafa dankon zumunci da sasanta tsakanin 'yan kasa.