Gabon: An koma gidan jiya bayan gasar kwallon kafa | Siyasa | DW | 06.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gabon: An koma gidan jiya bayan gasar kwallon kafa

Dokin gasar kwallon kafar Afirka ya kawo karshe, Kamaru ta ci kofin. Yanzu hankali ya karkata ga sanin rawar da gasar ta taka kan tattalin arziki da siyasar kasar.

Shugaba Ali Bongo na kasar Gabon ya so yin amfani da gasar AFCON don daga martabarsa

Shugaba Ali Bongo na kasar Gabon ya so yin amfani da gasar AFCON don daga martabarsa

Mahukuntan kasar ta Gabon mai kunshe da mutane miliyan daya da dubu dari takwas sun dauki nauyin shirya gasar cin kofin kwallon kafar na wannan shekara ta 2017 da kwadayin samun kudaden shiga. Su kuma 'yan adawar kasar na kallon wadannan wasanni a matsayin wata dama da shugaba Ali Bongo ke son yin amfani da ita wajen farfado da martabarsa a idon duniya bayan da a cewarsu ya kwace sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 27 ga watan Agustan bara. Wannan ce ta sanya tun tashin farko dai madugun 'yan adawa mista Jean Ping da wasu kungiyoyin 'yan fafutika na kasar ta Gabon suka yi kira ga 'yan kasar da suka kaurace wa filayen wasa a lokacin gasar domin nuna wa duniya adawarsu da matsayin shugaba Ali Bango. Kuma ba shakka wannan kira na 'yan adawa ya yi matukar tasiri inda akasarin filaye suka kasance tangwaza-gwaza a lokutan wasannin. Jean Remy Yama shugaban kawancan kungiyoyin kwadagon kasar ta Gabon ya yi karin haske kan wannan batu yana mai cewa.

Jean Remy Yama shugaban kungiyar kwadagon Gabon

Jean Remy Yama shugaban kungiyar kwadago ta Dynamique Unitaire a Gabon

"Gasar CAN ta fuskanci kalubale na siyasa da na tattalin arziki, kuma matsalar ta taso ne daga yadda gwamnati ta zabi zuba makudan kudade a cikin harkokin wasanni, a daidai loakcin da fannoni kamar na ilimi da kiwon lafiya ke fama da matsaloli. Har ta kai mata na haihuwa a kasa kazalika yara na daukar darasi a kas, an like jami'a tsawon watanni bakwai da sunan za a yi gyare-gyare da ba wanda ya gansu a kas. Don haka jama'a na jin haushin ganin irin yadda aka fi mayar da hankali kan wasanni, alhali ba a biya bukatunsu na yau da kullum ba. Kun ji kuma ai abin da kungiyar Tarayyar Turai ta fadi. Kazalika kun ji kiran da shugaba Ping ya yi wa 'yan kasa na su shirya shiga gwagwarmaya, kuma sun shirya. Don haka daga yanzu duk umurnin da ya bayar jama'a za su zartar."

Likkafar wasu ta yi gaba a sakamakon gasar ta AFCON

Tun a zagayen farko na gasar ne dai aka cire kungiyar kwallon kafar kasar ta Gabon daga cikin gasar bayan da ta kasa tabuka komi. Kuma abin mamaki an ga yadda wasu 'yan kasar da dama suka yi ta nuna farin cikinsu dangane da korar kungiyar tasu.

Gabun Librevile Oppositionsführer Jean Ping (DW/A. Kriesch)

Jagoran 'yan adawa Jean Ping wanda 'yan kasar da dama ke jin maganarsa

To sai dai daura da rigingimu na siyasa kananan 'yan kasuwar kasar da dama ne suka ja zaransu a lokacin gasar. Mme Bioguy mai sayar da abinci bakin filin wasa na birnin Libreville na daga cikin wadannan mutane da suka caba a lokacin gasar inda ta ce tana yin cinikin har jika dari na kudin CFA a yini.

"Ni kam ba zan yi korafi ba domin tun da aka fara wannan gasa ina samun karin kudaden shiga, wadanda nake kula da iyalina da su."

Wani sakamkon wucin gadi dai da kwamitin shirya gasar cin kofin kwallon kafar ta 2017 ya nunar da cewa kasar ta Gabon ta kashe biliyan 192 na CFA kwatankwacin miliyan 300 na Euro a shirya gasar. Sai dai 'yan adawa na cewa kudin sun kai biliyan 463 na CFA. A yanzu dai 'yan kasar sun kasa kunne su ji irin ribar da kasar ta samu a cikin shirya wasannin wadanda kasar ta shirya da nufin samar da kudaden shiga da za su taimaka ga farfado da tattalin arzikin kasar mai tangal-tangal.

Sauti da bidiyo akan labarin