Gaɓa Mafi amfani ga Mutum | Amsoshin takardunku | DW | 15.01.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Gaɓa Mafi amfani ga Mutum

Bayani akan gaɓoɓi guda biyar da suke isar da sako ga Dan-adam

Hoton Kan Mutum

Hoton Kan Mutum

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga Hannun Malam Iliya Kabiru daga garin Maradi a Jamhuriyar Niger. Malamin cewa ya yi, Shin, daga cikin gabobi guda 5, da suke isar da sako ga Dan-adam, wace gaba ce ta fi cika da kamala, kuma ta fi amfani ga Dan-adam?

Amsa: Abune sananne cewar,Dukkanin bayanan da muke dasu akan duniyar da muke rayuwa a ciki, Yana zuwar mana ne ta gabobi biyar. Wato Duniyar da muka sani; ta kunshi abinda idanmu yake gani, hannunmu yake tabawa, hancinmu yake shaka, harshenmu yake dandanawa, kuma kunnenmu yake ji. Bamu taba tunanin cewa akwai “wata duniyar” a waje, wadda wadannan gabobi zasu iya riskar damu ba, kamar yadda muke dogara dasu tun daga lokacin da aka haife mu.

Sabodahaka abune mawuyaci a iya cewa ga gabar da tafi karfi ko tafi amfani ga Dan-adam daga cikin wadannan gabobi guda 5.Babu shakka, bincike na kimiyya a yanzu ya kara tabbatar mana da cewa, sukansu wadannan gabobi suna dogaro ne da wani sako da aka suranta a kwakwalwarmu, ta hanyar naurar sakonni. Bari dai mu fayyace wannan bayani sosai yadda masu sauraro zasu fahimta.

Gani yana samuwa ne ta kyakkyawar hanya. Zirin haske (photons) wanda yake daga abin gani izuwa ido, yana shigewa ne ta fuskar idon, inda yake kakyaryewa, sannan ya fada bai bai akan tantanin ido wanda yake bayan ido Wanda ake kira da suna Retina a turance.Anan ne ake sarrafa hasken daya shiga ya zama na,urar sakonni, wadda take aika sakonni ta kwayar ido zuwa wani dan-kankanin bigire wanda ake kira cibiyar maganai, a bangaren baya, na kwakwalwa. wannan na’urar sakonni,ana riskassa kamar hoto a cibiyar magudanai a kwakwalwa, bayan tafiyar matakai. A hakika gani yana gudana ne a wannan dan-kankanin bigire a can bangaren kwakwalwa.

Yanzu, bari mu sake duban wannan al’amari da yanayin gudanarsa. Idan muka ce “muna gani”,duk abin da ka kalla din, kafin ka ganshi, sai naurar sakwanni ta je ta gayawa kwakwalwa cewar, wane ya tsinkayi abu kaza, sannan kwakwalwa ta suranta maka shi, har ka ganshi a surar da kake iya ganinsa.wato maana, idan muka ce “muna gani”, lallai muna ganin tasirin hasken dake fitowa ta idanunmu wanda yake tunkudowa daga kwakwalwarmu bayan ya canza kama zuwa na’urar sakonni.kuma wani ikon Allah shine ,duk da cewa muna gani ta hanyar tasirin haske daga umarnin kwakwalwa, kuma muna ganin Duniya, cike da launuka a cikin kwakwalwarmu.amma kuma babu komai a cikin kwakwalwa sai duhu. Wannan ba komai bane illa mu’jiza,daga Ubangijin da ya halicci gani.

Haka wannan lamari yake a dukkan sauran gabbanmu. Sauti, dandano da shakar kamshi duk suna tafiya ne zuwa kwakwalwa a matsayin na’urar sakonni da tsinkayuwa ta cibiyoyinsu a cikin kwakwalwa.

Gabar ji tana aiki ne ta irin wannan yanayi.wajen kunne shine yake daukar sauti daga makalutinsa, ya shigar dashi kai tsaye zuwa tsakiyar kunne; sannan kuma daga tsakiya zuwa can ciki inda za’a tace shi, sannan daga ciki ne za’a aiko da kadawar sauti zuwa kwakwalwa ta hanyar fassarasu zuwa na’urar sakonni. Kamar dai ido, hanyar ji ko sauraro tana gudana ne a cibiyar majiya a cikin kwakwalwa. Sauti na riskuwa ne a cikin kwakwalwa kamar yadda haske ya keyi. Saboda haka komai yawan karar da mutum yake ji a wajen, cikin kwakwalwa kuwa babu komai sai shiru.Koda yake har ma sautin da yafi kowanne rashin kara ana tsinkayarsu a kwakwalwa. Wannan shi yake tabbatar mana da cewa kunnen mutum mai cikakkiyar lafiya na iya jin komai ba tare da wani abu ya kawo cikas ga hakan ba. A kwakwalwarka inda sauti ke riskuwa, kake saurarar kukan tsuntsu, kake jin dukkan sautuka daga manisancin wuri, tun daga murmushewar ganye har izuwa karaj jirgin sama.

Fahimtarmu akan shakar kanshi ko wari, tafarkin daya ne da wadancan. Sunadaran da ake kira volatile a Turance,Sune suke fitowa daga abubuwa kamar turare, ko fure, ko masai ko kwatami, wato suna riskar jijiyoyi ne, dake zuko kamshin ko warin, suna aiwatar da wannan kai- kawo, daga nan ne kuma yake tafiya cikin kwakwalwa a siffar na’urar sakonni, sai ya karbe shi a matsayin kamshi. Duk abinda muke shaka, mai kamshi ne ko mai wari, ,ba komai bane illa kai- kawan daya faru ga kwayoyin sunadarai har suka isa cikin kwakwalwa ta hanyar canza shi izuwa siffar na’urar sakonnin a kwakwalwa, wanda kanyi kamshin turare, ko fure ko warin kashi ko zarnin fitsari . Muna iya cewa, dukkanin kamshin da mutum ke iya zaton yaji tun lokacin da aka haife shi ba komai bane, illa naurar sakoni da yake riska ta wadannan gabobi.

Dangane da dandano da muke riska ta harshen mu, akwai rabe – rabe guda hudu tattare da sunadarai a farkon kashi na harshen mutum. Wadannan suna kunshe ne da raben – raben dandanon zartsi, zaki, daci, da tsami, bauri da dai sauransu. Wadannan sunadarai, sune suke rikida da zaton dayan wannan zuwa naurar sakonni, daga nan sai a tura su izuwa kwakwalwa.Wadannan na’urori ana riskar su a kwakwalwa a matsayin dandano.Dandanon dake zuwar wa mutum a lokacin da ya sha alawar zaki ko a dan-itacen da kayi sha’awa ai fassarar kwakwalwa ce ta hanyar naurar sakonni.Mutum bazai taba gani, shaka ko dandana alawar zaki ba kaitsaye daga kanta.

Anan ne aka fahimci cewa,babu wani dan-adam da yake jin dandano dai da da wani,ko ganin abu dai-dai da wani, ko kuma jin sauti daidai da wani.kowa yana tsinkayar nasa ne daban.

Gabarmu ta tabi bata da bambaci da sauran.Idan muka taba wani abu, dukan bayanin da ka iya taimakawa mu fahimci bayanin abinda muka taba,ana tarawa ne a kwakwalwa ta jijiyoyin dake fatar jiki. Sannan mutum yaji a kwakwalwar sa yana taba wani abu. Misali idan mutum ya taka garwashin wuta, to bazai ji wannan zafin wutar ba har sai naurar sakonni ta kai sakon ga kwakwalwa, tana mai sanar da ita cewa wane fa ya taka garwashin wuta, sannan ka tsinkayi zafin ta wani dan-kankanin bigire a cikin kwakwalwa wanda ake kira cibiyar jin-tabi. Sabodahaka a hakikanin gaskiya , inda muke tsinkayar tabi, ba yan-yatsunmu bane ko fatar jikimmu, a’a , a cibayar tabi ne a kwakwalwar mu, a sakamakon aikace – aikacen da na’urar dake aika sakonni tayi daga abin da aka tabawa zuwa ita, ta hakane muke jin yadda kowace gaba ke aikinta, akan abin da aka taba, kamar tauri ko laushi ko zafi ko sanyi ko kaushi ko dumi ko kaifi da dai sauransu.

Sakamakon dalilai na zahirin da muka kwatanta, zamu iya cika maganar mu da cewa,. Dukkan abinda muke gani, tabawa, ji, da tsinkaya a matsayin halitta”, na Duniya da abida ke cikin ta, ba komai bane illa na’urar sakonni wadda take gudana a cikin kwakwalwamu.

Wannan bayani da muka gama yanzu, yana daya daga mafi girman gaskiyar da mafiya yawan mutane basu taba sani ba,wanda kuma baa taba gaya maka a rayuwarka . Wannan shi yake tabbatar da cewa, rayuwar da ake gani a Duniya.”inuwar halitta”ce, wannan bayani shine mukullin da zai budewa mutum fahimtar wanzuwar ubangiji da kuma fahimtar cewa shine kadai mahalicci,wanzajje,kuma madawwami.Duk wani abu na Duniya, fararre ne kuma kararre ne,Allah madaukakin sarki shine kadai ya tabbata wanzajje.

Adadin mutanen da suka fahimci wanan hujja basu da yawa a tarihi; Saboda wannan dalili ne, karai ne 21 zai zama wani yanayi na kawo sauyi a tarihi, a yayin da mutane zasu fahimci hakikanin hilitta, kuma a fahimtarda su izuwa Allah, kadaitaccen zati, Dan-adan zai yantu daga tsofaffin katangun, rudani da camfe –camfe dasuka dabaibaye shi .ya fahimci cewa, babu wani tabbataccen zati sai Allah,shine madaukakin sarki, mabuwayi kuma mai hikima, kuma mahaliccin komai.

Allah shine mafi sani.

 • Kwanan wata 15.01.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvV2
 • Kwanan wata 15.01.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvV2