G5 Sahel ta yi tir da sanya mata harin kunar bakin wake | Siyasa | DW | 09.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

G5 Sahel ta yi tir da sanya mata harin kunar bakin wake

Kungiyar mata ta kasashen yankin Sahel karkashin inuwar G5 Sahel a taron koli da ta gudanar a kasar Niger ta baiyana damuwa yadda kungiyoyin ta'adda ke amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake.

Sahel: G5 ta koka kan amfani da 'yan mata wajen kai hare-haren ta'addanci.

Sahel: G5 ta koka kan amfani da 'yan mata wajen kai hare-haren ta'addanci.

Mata wakilai daga kasashe biyar na yankin sahel da suka hada da Chadi da Moritaniya da Mali da Burkina Faso da kuma Niger mai masauki a karkashin kungiyar  G5 Sahel sun yi nazarin matsalolin tsaro da suka addabi yankin da kuma hanyoyin da za a bi domin kawo karshen matsalar.

Musamman kungiyar ta nuna matukar damuwa kan yadda kungiyar Boko Haram ke amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake da lalata musu rayuwa

Madam Habibu Hasiya Issa, jami'a a hukumar kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya ONU ta yi tsokaci kan yadda irin wadannan kungiyoyin ta’adda ke sace yara 'yan mata kanana suna yi musu fyade da kuma sanya su harin kunar bakin wake inda suke salwantar da rayuwarsu da ta sauran jama'a.

A nata bangaren wakiliyar kasar Chadi, Madam Appoli Motalbai babbar sakatariya a ofishin ministan matan kasar, ta ce akwai babban kalubale a gaban al’umma, inda ta bukaci kowa ya bada gundunmawarsa wajen inganta tarbiyyar yara domin ganin basu shiga cikin kungiyoyin bata gari ba.

Ita ma da take tsokaci Dr Joustie Koulidiatie, wakiliya daga  Burkina Faso ta baiyana damuwa yadda ta ce ake mayar da mata saniyar ware a al’amuran raya kasa, tana mai cewa mata su ne ginshikin al’umma a saboda haka akwai bukatar damawa da su a dukkan al’amura na ci gaban kasa.

Sauti da bidiyo akan labarin