Fyade wa kananan yara a kudancin Sudan | Labarai | DW | 03.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fyade wa kananan yara a kudancin Sudan

Rahotannin da jaridar Daily telegraph din london ta yayata na nuni dacewa dakarun kiyaye zaman lafixya na mdd da maikatan gaji dake aiki a kudancin sudan na yiwa yara kanan da shekarun su basu shige 12 da haihuwa ba Fyade.Jaridar ta rahotanta data yayata ta yanar gizo gizo,nacewa tanada shaida daga sama da yara mata 20 dake garin Juba ,da maaikatan mdd suka tilstasu ta hanyar fyade.Jaridar ta kara dacewa ,irin wannan taassar na kunshe cikin wani rahoto da hukumar kula da kanan yara ta Unicef ta gabaratar watanni kalilan da isnan dakarun mdd a kudancin Sudan a watan Maris na 2005.Damien Personnaz shine kakakin Asusun UNICEF.