1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fuskokin waɗanda suka taimaka wajen shirya shirin na Ji Ka Ƙaru

Bashir, AbbaMay 14, 2008
https://p.dw.com/p/DrHz
Hoto: DW/Ahmed-Zainab Mohammed

Fuskokin waɗanda suka taimaka wajen shirya shirin na Ji Ka Ƙaru.

Sun zo daga ko’ina daga ƙasashen Afirka, sun ƙunshi ‘yan jarida da suka daɗe a aikin, matasa masu son su koyi aikin jarida, rubuce-rubuce waɗanda suke da sha’awar a dama da su a ko yaushe. Ga wasu daga cikin waɗanda suke taimakawa wanzuwar shirin:

Hope Azeda ƙwararriya ce a wajen shirya waƙoƙi kaɗe-kaɗe da raye-raye da yaɗa labarai. ‘yar ƙasar Rwanda ce, mai sha’awar rubuce-rubuce musamman akan al’amuran da suka shafi zamantakewa, baya ga haka tana mai ba da shawara ga ƙungiyoyi masu zaman kansu, tana da takardar shaidar Diploma a fannin kaɗe-kaɗe da raye-raye daga Jami’ar Makerere.

Justine Bitagoye kuwa ta fara aikin jarida ne da Talabijin a matsayin mai gabatarwa a ƙasarta ta haihuwa wato Burundi. Ta yi fice a gasar nuna finafinai na ƙasashen Afirka inda ta ja hankali da wani shiri da ta yi, akan wasu yara marasa galihu. Justine ma kamar Hope ta yi karatunta ne a Jami’ar Makerere kuma tana da takardar shaidar digiri na biyu, tana aikowa shirin Ji Ka ƙaru rahotanni akan gurɓatar yanayi a duniya.

Alex Billy Gita ɗan ƙasar Uganda, sabon jinin ɗan jarida ne, a duk lokacin da baya da wani rahoto da zai aikawa shirin Ji Ka Ƙaru to ka neme shi a can Gidan Rediyon Uganda, yana ɗauke da rahotanni da ɗimi ɗiminsu . ya samu horon fannin Jarida a Institute of Mass Communications, sannan ya samu horo ta hanyar kwasa-kwasai a gidajen radiyon BBC da Deutsche Welle.

Christine Harjes ‘yar ƙasar Jamus ce, ta sha mafarkin barin ƙasarta ta haihuwa tana son fita waje, ba inda taso kamar nahiyar Afirka. tana aikowa Radiyo Deutsche Welle rahotanni daga Uganda, Kenya, Rwanda, da Burkina Fasso. A yanzu haka ita ce babbar manaja mai kula da shirin Ji Ka Ƙaru.

Pierre Kazoni ɗan ƙasar Burkina Fasso, mutum ne mai son abubuwa biyu, koyarwa a aji da kuma aikin jarida. Ya koyar da darasin Turanci a makarantu da dama a ƙasar Burkina Fasso, a wannan lokacin yana haɗawa da aikin jarida a Gidan Rediyo da Telebijin na ƙasa. Yana alfahari da waɗannan ayyuka nasa.

Sam Tolulope Olukoya sanannen ɗan Jarida ne a Najeriya, yana aiki ne a rediyo da telebijin har ma da jarida inda ya yi fice saboda rubuce-rubucensa akan irin gwagwarmayar garin Lagos, ya samu kyaututtuka na iya rahotonni a radiyo da jarida. Sam na so ya ga matasa sun yi fice a duk abin da suka zaɓa na rayuwa.

Zainab Aziz Salim kuwa, barin ƙasarta ta haihuwa Kenya ta yi, shekaru huɗu da suka wuce, ƙwararriyar ‘yar jarida ce, ta yi aiki a Gidan Rediyon Kenya da kuma sashen Kiswahili na Rediyo Deustche Welle, tana mai alfaharin aikawa shirin Ji Ka Ƙaru rahotanni akan ci-gaban nahiyar Afirka.