1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

FUSKANKUNGIYYAR EU A SHEKARA TA 2004 DA KUMA KALUBALEN DA ZATATA A SHEKARA TA 2005.

TUTOCIN KASASHEN KUNGIYYAR TA EU DAKE KAKKAFE A BABBAN OFISHINTA DAKE BRUSSELS

default

A yayin da kasashen duniya ke shirye shiryen yin ban kwana da shekara ta 2004 da kuma murnar shiga sabuwar shekara ta 2005 a dai dai lokacin ne kungiyyar tarayyar turai ke murnar samun sauki na karewar wan nan shekara a hannu daya kuma da tunanin irin manya manyan kalubalen da kungiyyar zata fuskanta a cikin sabuwar shekarar.

A misali rahotanni sun nunar da cewa kungiyyar ta Eu a shekara ta 2004 ta samu kanta a cikin wani mawuyacin hali na kaka ni kayiv kama dai daga daukar matakin karta yawan yayan ta daga 15 izuwa 25 da kuma tataburza da aka sha game da kundin tsarin mulkin kungiyyar a majalisar dokoki da kuma musayar miyau da aka sha game da nadin sabbin kwamishinonin wan nan kungiyya.

Har ilya yau akwai kuma batun matakin da kungiyyar ta Zartar na yaki da aiyukan yan taadda da kuma taaddanci a doron kasa. Hakan kuwa ya samo asali ne kwanaki kadan bayan Harin kunar bakin waken nan na Birnin Madrid da yayi sular mutuwar mutane 191 ban da wasu da yawa kuma da suka jikkata.

Bugu da kari a karshen shekarar ta 2004 shugabannin kungiyyar 25 na Eu sun kare zaman nasu ne a can Bienin Brussels tare da amincewa da bude kafar fara tattaunawar kasar Turkiyya a cikin ta a watan oktoba na shekara ta 2005.

Rahotanni dai sun nunar da cewa duk da wadan nan matakai naci gaba da kungiyyar ta Eu ta samu damar aiwatarwa a cikin shekara ta 2004, akwai kuma wasu manya manyan kalubalen dake gabanta a cikin sabuwar shekarar ta 2005 da suka kama daga harkokin siyasa da kuma tattalin arziki.

Wani kuma kalubalen da kungiyyar ta Eu zata fuskanta shine na kokarin janyo hankalin yayan ta game da alkiblar da kungiyyar zata dosa a shekara ta 2005 din,musanmamma bisa la,akari da cewa cikakkiyar tattaunawa game da kundin tsarin mulkin kungiyyar za a fara shine a sabuwar shekarar ta 2005.

Bugu da kari a hannu daya kuma akwai bayanin cewa yayan kungiyyar zasu ci gaba da tattauna yiwuwa ko kuma akasin hakan na karbar wasu klasashen a cikin ta a dai cikin wan nan sabuwar shekara ta 2005.

Wadan nan kasashe kuwa sun har da Romania da Bulgeria da Croatia da kuma ita kanta kasar ta Turkiyya.

Game kuwa da harkokin siyasa ta kasa da kasa ana sa ran kungiyyar ta Eu a cikin sabuwar shekara zata sa ido game da harkokin zaben shugaban kasa a Iraqi da kuma Yankin Palasdinawa a hannu daya kuma da duba yiwuwar cirewa kasar Sin takunkumi na hana mata sayen makamai da aka garkama mata na tsawon shekaru 15.

Har ilya a cikin sabuwar shekarar kungiyyar gamayyar ta turai za kuma ta taci gaba da daukar matakan dinke barakar dake akwai a tsakanin wasu yayan ta da kasar Amurka. Babban batu game da wan nan shine na yadda kungiyyar ta Eu zata shirya wani taron koli da ake sa ran halartar shugaba Bush a watan fabarairun sabuwar shekarar ta 2005.

Ibrahim Sani.