Fushin Kasashen Afirka kan Indiya | Labarai | DW | 03.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fushin Kasashen Afirka kan Indiya

Kyamar da 'yan Afirka ke fuskanta a kasar Indiya janyo martanin kasashen Afirka inda suka yi Allah wadai gum din da Indiya ke yi kan wannan batun.

Anschlagsserie im Kaschmir-Gebiet 11.07.2006 Touristen getötet (AP)

Kasashe 44 na nahiyar Afirka, sun zargi kasar India kan kin hana hare-haren nuna kyamar da indiyawa suka nunawa 'yan kasashen Afrika, musamman 'yan Najeriya da ke kasar. Mutane da dama ne dai suka sami raunuka, wasu ma munana, bayan afkawa baki bakar fata da indiyawa suka, sakamakon mutuwar wata yarinya a birnin Delhi ranar Litinin na makon jiya.

Rigimar dai ta tashi ne bayan sakin wasu 'yan Najeriya da aka zarga da hannu cikin mutuwar yarinyar. Wata sanarwar da shugabannin na Afirka suka fitar, sun yi matukar nuna damuwa ne da rashin samun bayanan jaje ko nuna nadamar aika-aikar daga mahukuntan kasar ta Indiya.