Fursunonin Morokko | Labarai | DW | 27.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fursunonin Morokko

ƙungiyoyi dake fafutukar kare hakkin bil’a dama na ƙasar Morokko, sun yi Allah wadai da mawuyacin halin da wasu fursunonin musulmi su 360 ke ciki a gidanjen kurkuku dake war-watse a ƙauyuka kusa da babban birnin ƙasar. Kungiyoyin sun yi kira da a dauki matakan gaggawa wajen tabbatar da an kare mutuncin wadannan fursunonin. A wani rahoton da sunka gabatar a yau, ƙungiyoyin da suka ziyarci fursunonin, sun bayyana takaici game da halin da suka sami furzunonin musulmi a ciki. Tuni daruruwan fursunonin suka shiga yajin aiki da niyar janyo hankalin duniya kann mawuyacin hanlin da suke ciki. Kungiyoyin kare hakin bil’adaman, sun tsara wasu matakan da gwamnatin Morocco zata iya dauka wajen kawo karshen wannan cin mutunci da azaba da jami’an tsaro ke gallazawa fursunoni musanman musulmi da suke tsare.