Fursunoni sun kashe kansu a Guantanamo | Labarai | DW | 11.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fursunoni sun kashe kansu a Guantanamo

Wasu fursunoni 3 sun rataye kansu a gidan fursunan Guantanamo dake karkashin Amurka.

Kungiyoyin kula da kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun baiyana cewa,fursunono 3 da suka rataye kansu a gidan gwale gwale na Guantamo sunyi hakan ne saboda sun fidda rai daga fita daga gidan fursunan dake karkashin kulawar Amurka.

Kungiyoyin na kare hakkin jamaa suka ce fursunoni da dama sun gudanar da yajin kin cin abinci da dama kuma sukayi kokarin kashe kawunansu,saboda basu hango karshen zamansu gidan fursunan na Guantanamo ba tare da an caje su ba.

Shugaba Bush na Amurka dai ya baiyana abinda ya kira matukar damuwa dangane da mutuwar wadannan mutane uku,wadanda suka hada da yan kasar saudiya 2 da dan kasar Yemen daya.