1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Frankreich D. Europa

Yahouza, SadissouJune 15, 2008

Matsayin haɗin gwiwar Jamus da France a Ƙungiyar Tarayya Turai.

https://p.dw.com/p/EK5t
A.Merkel da N. sarkozy manyan EUHoto: AP Graphics/DW

Masu sauraro a salamu alaikum barka mu da warhaka lale marhabin da sake saduwa daku a wani saban shiri na duniya mai yayi, shirin da kan gabatar maku da bayyanai, a game da al´ammuran da suka shafi siyasa da kare haƙƙoƙin bani adama a sassa dabam dabam na duniya.

A wannan karo , shirin zai duba matsayin haɗin gwiwar ƙasashen Jamus da France, a harakokin gudanarwa na Ƙungiyyar Tarayya Turai.

Nine Yahouza Sadissou Madobi ke farin kasancewa tare da ku.


Yau shekaru fiye da 50 kenan ƙasashen Turai suka ƙaddamar da wani shirin haɗin kai a tsakanin su, wanda sannu a hankali ya kai ga girka Ƙungiyar Tarayya Turai, wato EU.

Kasashen Jamus da France sun taka muhimmiyar rawa, wajen girka wannan Ƙungiyar wace  a halin da ake ciki ta ƙunshi ƙasashe 27.

Kamar yadda ƙila kuka sani, a lokacin yaƙin duniya na biyu, tsakanin shekara ta 1939 zuwa 1945, Jamus da France sunyi mummunar gwabzawa, to saidai bayan lafawar ƙura yaƙi, ƙasashen biyu, suka yanke shawara haɗa ƙarfi, domin girka wata babbar ƙungiya da zata haɗa kan Turai da zumar riga kafi ga abkuwar masifa tsakanin su, irin  ta yaƙin duniya na biyu.

Jannar Charles Degaulle shugaban ƙasar France a bayan yaƙin, ya kawo ziyara farko a nan ƙasar Jamus a yunƙurin cimma wannan buri.

Albarkacin wannan rangadi na Dagaulle a ranar 04 ga watan Satumba na shekata ta 1962, Shugaban ƙasar Jamus ta yamma na lokacin Dr.Lübcke Henrich a jawabin da ya gabatar, yace daga wannan rana ƙasashern biyu, sun gafarci juna, a game da abubuwan da suka wakana a baya, ya kuma cigaba da cewar:

" Fransawa da Jamusawa sun gwabza yaƙi, amma a yanzu sun girka tubalin tushe ,na samar da zaman lafiya mai ɗorewa, ƙasashenmu  sun ƙudurci haɗa ƙarfi domin ciyar da al´ummominsu gaba, ta fannonin al´adu ,kimiya, fasaha tattalin arziki da sauran al´ammuran rayuwa.

Muna fata kar Allah ya maida sau baya.

A yau France da Jamus, sun amince su gama kai ta hanyar cuɗe ni in cuɗe ka, domin gina kyakkyawar makoma ga al´ummomi.

Bugu da ƙari zamu amfani da wannan saban haɗin kai, domin mu ƙarfafa mu´amila tsakanin ƙasashen  turai baki ɗaya.

A shekara ta 1950 aka yanka ragon sunan Ƙungiyar Tarayya Turai, an cimma wannan matasayi  a dalili da haɗin kai da fahintar juna tsakanin Jamus da France" .

A yayin da yake nasa jawabi shugaba Jannar Charles Degaulle na France ya jadada imanin mahimmancin hulɗoɗi tsakanin Jamus da France wanda sune ƙasashen dake matsayin shika shikan dake tallabe da Ƙungiyar Tarayya Turai, duk kuwa da matsalalolin da ake cin karo da su.


" Akwai matsaloli dabam dabam, daga waje, da cikin gida, wanda ke tattare da yunƙurin kafa Ƙungiyar Tarrayya Turai, to amma Jamus da France sun riga sun amince da girka wannan Ƙungiya, saboda haka, ba zamu ƙasa a gwiwa ba, domin ganin Ƙungiyar ta zauna da gindinta.

Cimma wannan buri babu shakka, babban taimako ne ga Nahiyar Turai baki ɗaya da kuma zaman lafiya  a duniya."


Tubalin haɗin kai da Shugaba Dagaulle na France da shugaban gwamnatin Jamus Konrad Adenauer suka girka, ya samu karɓuwa daga shugabanin da suka biwo bayan su da ma al´ummomin ƙasashen biyu.

Wannan haɗin kai yayi matuƙar tasiri wajen shinfiɗa dokoki da tsarin mulkin ƙungiyar Tarayya Turai.

A dangane da haka, bayan haɗewar Jamus ta gabas da Jamus da yamma shugaban ƙasar France Jacques Chirac shine na farko da Majalisar dokokin Bundestag ta gayyata, inda ya gabatar da jawabi a game da wajicin ƙarfafa haɗin kai tsakanin Jamus da France.

Chirac ya ƙara da cewa:

" Fiye da duk sauran ƙasashen duniya, Jamus da France sun yi imani da zaman lafiya da haɗin kan ƙasashen Turai.

Wannan ƙasashe su biyu kaɗai, na da ƙarfi da kuma kyakkyawar aniyar tabbatar Turai a matsayin dunƙullaliyar Nahiya.

A sakamakon aniyar al´ummominmu biyu, Ƙungiyar EU ta samu cigaba.

Jamus da France, sun yi abun a zo a gani wajen bunƙasa Ƙungiyar Tarayya Turai".

Duk da tasirin Jamus da France a cikin tafiyar  EU, wannan Ƙungiya na cin karo da matsaloli iri iri, hasali ma a game da abunda ya shafi kudin tsarin mulkinta, wanda har yanzu ake cigaba da kai ruwa rana a kansa.

Idan ba a manta ba, al´aummomin ƙasar France a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2005 suka yi watsi da wamnnan kundi  a sakamakon zaɓen raba gardama da suka shirya,  a yayin da itakuwa Majalisar Dokokin Bundestag ta Jamus ta bayyana amincewa da shi.

Duk da wannan saɓanin da aka samu, shugaban ƙasar France,Nikolas Sarkozy kwanaki kaɗan bayan zaɓen sa a wannan matsayi, ya kawo ziyara aikinsa ta farko a ƙetare, inda ya fara da fadar mulkin birnin Berlin.

Yayi amfani da wannan dama, domin dabatarawa shugabar gwamnati Jamus Angela Merkel wannan jawabi:


" Har abada babu abunda zai kawo cikas ga mu´amilar da aka ƙulla tsakanin Jamus da France, bayan matsaloli mummuna da ƙasashen suka yi fama da su."

A sakamakon ganawa tsakanin Merkel da Sarkozy, Jamus da France suka yanke shawara gudanar da kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin Ƙungiyar Tarayya Turai, ta yadda zai samu karɓuwa daga ƙasashe membobi baki ɗaya.

Sun cimma wannan buri  a taron Lisbonne na ƙasar Portugal, inda baki ɗaya shugabanin ƙasashe ko na gwamnatocin EU, suka rattaba hannua kan wani taƙaitacen kudin tsarin mulki, da aka raɗawa suna yarjejeniyar Lisbonne.

To saidai  bayan da Majalisun dokokin ƙasashe  18 sun amince da wannan saban kudin, sai kwatsam !!! kamar daga sama, al´ummumoin Irland suka yi watsi da shi a sakamakon zaɓen raba gardama da suka shirya kansa.

Kamar yadda dokokin EU suka tanada, ya zama  wajibi a samu amincewa 100%  daga ƙasashen membobin baki ɗaya kamin doka ta fara aiki.

Wannan sabuwar baddaƙƙala ta wakana a yayin da ya rage ´yan kwanaki ƙalilan France ta karɓi jagorancin Ƙungiyar Tarayya Turai.

Saboda haka yauni ya rataya a kan Paris da Berlin tare da haɗin kan sauran ƙasashen EU su gano tudun dafawa.

Tuni dai Jamus da France dake riƙe da sitiyarin EU, sun fiddo sanarwar haɗin gwiwa, inda suka bayyana takaici a game da matakin da Irland ta ɗauka, tare da ɗaukar aniyar laluba hanyoyin fita daga wannan sabuwar dambarwa, kamar yadda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana.


" Jama´ar Irland sun zaɓi yin watsi da wannan kundin tsarin mulki.

A matsayin mu na masu kishin turai sai mu yi amfani da wannan sakamako, domin mu duƙufa wajen neman mafita, ba tare da ƙin amincewa da zaɓinsu ba."

Ƙaramin minista mai kulla da harakokin  Turai na gwamnatin ƙasar France Jean Pierre Jouyet, ya bayyana matsayin Jamus da France a dangane da kuri´ar amincewa da Irland ta kada.

"Abu mafi mahimmanci shine sauran ƙasashen su cigaba da kaɗa ƙuri´a, a game da kundin.

Sannan a ƙarshen zaɓɓuɓukan, sai mu zauna tare da gwamnatin Irland, mu saurareta, mu gano baki ɗaya wace hanya zamu iya bi a cikin tsarin doka, domin cimma masalaha."

A halin da ake ciki dai tunni ƙasashe 18 wanda suka hada da Jamus France Poland da Portugal sun kaɗa ƙuri´ar amincewa da wannan kundi.

Bayan ƙin amicewar Irland, ya ragewa ƙasashe takwas su bayyana matsayinsu.

Shugaban gwamnatin  Engla Gordon Brown ,yace duk da watsi da jama´ar Irland tayi da kundi, Engla za ta ƙuri´a kansa.

Saidi dai koda sauran ƙasashen su shirya wannan ƙuri´a, akwai matuƙar wuya a fara amfani da kudin, ranar 1 ga watan Janairun shekara mai kamawa kamar, yadda aka tsara da farko.