1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Frank-Walter Steinmeier zaije yankin gabas ta tsakiya

Zainab A MohammedAugust 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5x

Ministan harkokin waje na Jamus Frank-Walter Steinmeier,na kann hanyarsa ta zuwa rangadin aiki ,karo na uku acikin tsukin wata guda,inda akesaran zai bukaci shugabanin yankin su taimaka wajen tabbatar ingantacciyar zaman lafiya mai dorewa a tsakanin Izraela da yan Hizbollah.Sanarwar data fito daga maaikatar harkokin waje a Berlin na nuni dacewa,Mr Steinmeier,zai fara yada zango ne a a kasar jordan,kana a gobe talata zai isa syria,kana zai kammala rangadin aikin nasa da kasar saudi Arabia,a ranar Laraba da yammaci.Anasaran cewa ministan harkokin wajen na Jamus ,zai bukace kasashen dasu taka rawar gani,akokarin da kasashen duniya keyi na ganin cewa an gano bakin zaren warware rikicin,musamman kasar Syria,wadda tace tana marawa yan Hizbollah baya.Izraela da Amurka dai na zargin Damascus,da samarwa mayakan kungiyar makamai.