France da Britania sun bayyana sanarwar haɗin gwiwa a game da rikicin Darfur
July 27, 2007A wata sanarwar haɗin gwiwa, ministocin harakokin wajen France da na Engla, sun yi kira ga gwamnatin Sudan da yan tawaye su mutunta yarjeniyoyin zaman lahiar da a ka cimma tsakaninsu.
Ƙasashen 2 sun cimma daidaito, a game da batun haɗa ƙarfi da husa´o´i, domin magance rikicin yankin Darfur.
Sanarwar ta Bernard Kouchner da David Miliband, ta ƙasashe France da Britania, na aiki kafaɗa da kafaɗa a Majalisar Ɗinkin Dunia da zumar aika rundunar shiga tsakani cikin gaggawa.
A ɗaya ɓangaren,
komitin mussamman na Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kulla da kare haƙƙoƙin bani adama , ya yi suka da kakkausar halshe ga hukumomin Sudan, a game da tallafin da su ke baiwa mayaƙan Janjawid a yankin Darfur.
Komitin yayi Allah wadai ga wannan ɗabi´a ta gwamnati, wadda ya dangata da ƙabilanci.
Rahoton da komitin ya gabatar a yau juma´a, ya buƙaci hukumomin Khartum su daina bada talafi ga yan Jandjawid, sannan su gudanar da bincike, domin hukunta dukkan wanda a ka samu da hannu, a rurar wutar rikicin yankin Darfur.