Fraministan Italiya ya nemi ƙuri′ar amincewa da shi | Labarai | DW | 14.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fraministan Italiya ya nemi ƙuri'ar amincewa da shi

Silvio Berlusconi, fraministan Italiya ya nemi majalisun ƙasar su kaɗa ƙuri'ar amincewa da shi

default

Silvio Berlusconi, fraministan Italiya

Kwana ɗaya bayan da 'yan adawa suka yi yunƙurin tuntsurar da shi, fraministan Italiya Silvio Berlusconi ya ce zai nemi a kaƙa ƙuri'ar amincewa da shi a majalisar dokoki. Berlusconi ya aike wasiƙa ga shugabannnin majalisun ƙasar guda biyu, yana mai mika buƙatar kaɗa wannan ƙuri'a sakamakon sa hannu da yayi akan kasafin kuɗi da kuma gabatar da dokar samar da ɗorewar ci-gaba da ake muhawara akai a yanzu. Bayan kaɗa wannan ƙuri'a zai yi jawabi ga majalisar dattawa inda zai nemi a kaɗa ƙuri'ar amincewa da shi a majalisun guda biyu. Berlusconi dai ya lashi takobin ƙin sauka daga muƙaminsa ko da yake mai yiwuwa ne ba zai koma samun rinjaye a majalisa ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu