Florida:Jama′a na fargaba kan guguwar Irma | Labarai | DW | 09.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Florida:Jama'a na fargaba kan guguwar Irma

An umarci miliyoyin jama'a su fice daga jihar Florida yayin da guguwar Irma ke kara gabatowa

Hukumomi a jihar Florida ta Amirka ta umarci miliyoyin jama'a su gaggauta ficewa gidajen su yayin da mahaukaciyar guguwar Irma hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya ke cigaba da tunkarar jihar bayan ta yi mummunan ta'adi a Kuba inda ta hallaka akalla mutane 21 tare da jikata wasu da dama a gabashin yankin Caribbean.

Guguwar Irma wadda ke zama mafi karfi da aka taba gani cikin shekaru dari ana tsammanin za ta dira Florida a gobe Lahadi, inda ake hasashen za ta haddasa ta'adi mai yawa da kuma ambaliyar ruwa a jihar ta Florida mai yawan al'umma.

Gagarumin aikin kwashe jama'a wanda ya hada da wasu yankuna a Miami na fuskantar tarin matsaloli sakamakon cushewar hanyoyi da karancin man fetur da kuma kalubalen kwashe tsofaffi zuwa tudun mun tsira.

Mutane fiye da miliyan biyar da rabi ne aka umarci su bar gidajen su a Florida bisa alkaluman hukumar agajin gaggawa ta jihar.