Fiye da mutane 50 sun mutu a fashewar wasu bama-bamai 3 a birnin New Delhi | Labarai | DW | 29.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fiye da mutane 50 sun mutu a fashewar wasu bama-bamai 3 a birnin New Delhi

Akalla mutane 50 sun rasu sannan das dama sun samu rauni a wasu jerin hare haren bam da aka kai a New Delhi babban birnin Indiya. Da yawa daga cikin wadanda fashewar bama-baman ta rutsa da su dai mata ne da kananan yara. Kamar yadda hukumomi suka nunar bama-bamai 3 suka fashe mintoci kalilan bayan juna a cikin wasu kasuwanni dake cike da jama´a sai kuma daya da ya fashe a cikin wata safa. Daya daga cikin kasuwar ta na a wata unguwa ne da baki ´yan yawon shakatawa ke yawaita zuwa. Kakakin FM Indiya Manhoman Singh ya bayyana fashewar bama-baman da cewa wani aiki ne na ta´addanci. Kawo yanzu ba wanda yayi ikirarin hannu a hare-haren wadanda suka zo kwanaki 3 gabanin bikin ´yan Hindu da ake kira Diwali da za´a yi a ranar talata.