Fiye da mutane 200 sun rasa rayuka a Irak a cikin hare-hare | Labarai | DW | 15.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fiye da mutane 200 sun rasa rayuka a Irak a cikin hare-hare

A ƙalla mutane 200 su ka rasa rayuka, sannan wasu ɗaruruwa su ka ji mumuna raunuka, a sakamakon hare-haren ƙunar baƙin wake da su ka rutsa da birnin Bagadaza.

Hare-haren da su ka wakana yammcin jiya sun hadasa ruɗani ga rayuwar mazauna Ninive, yankin da abun ya faru.

Wannan na ɗaya daga mumuman hare-haren da yan takife su ka kai a Irak, tun bayan kifar da tsofan shugaban ƙasa, mirgayni Saddam Hussain a shekara ta 2003.

Ƙasar Amurika ta yi tur da Allah wadai ga wannan saban hari, wanda a cewar ta, ba zai karya mata ƙarfin gwiwa ba, a yunƙurin ta na samar da zaman lahia a ƙasar Irak.

Kazalika Britania babbar abikiyar ƙawancen Amurika a Irak, ta bayyana damuwa a game da hauhawar tashe-tashen hankulla a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Harin ya abku jim kaɗan bayan da wasu yan bigida su ka yi awan gaba, da mataimakin minsitan albarkatun man petur a opishin sa dake birnin Bagadaza.

Duk da tsatsauran matakai da Amurika ta ɗauka a ƙasar Irak, har yanzu an kasa gano haske a game da batun zaman lahia a wannan ƙasa.